35.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

“Na samu juna biyu” Cewar Ummi Rahab amaryar Lilin Baba

LabaraiKannywood"Na samu juna biyu" Cewar Ummi Rahab amaryar Lilin Baba

Amaryar shahararren mawaƙi, jarumi kuma furodusa a masana’antar Kannywood Shu’aibu Ahmed Abbas (Lilin Baba) kuma tsohuwar jarumar Kannywood, Rahama Saleh Ahmed (Ummi Rahab), ta sanar da cewa ta samu juna biyu.

Ummi Rahab ta bayar da wannan sanarwar ne a Instagram, inda ta saka hoton ta sanye da wata jar atamfa, ta na zaune a kan kujera ta na murmushi. Jaridar Fim Magazine ta rahoto.

Ummi Rahab da kan ta sanar da samun rabon da tayi

A saƙon da Ummi Rahab ɗin ta fitar ta rubuta da manyan baƙaƙe cewa:

“Ina ɗauke da juna biyu.”

Jarumar wacce ta bar fitowa a cikin finafinai tun bayan aurenta ta kuma yi kira ga masoyan ta da su taya ta murnar samun wannan abin arziƙin da tayi, inda har ta yi alƙawarin za ta bayar da tukwicin katin waya ga mutum 50 na farko da su ka tura saƙon murnar a ƙasan hoton nata.

A kalamanta:

“Idan na samu ‘comments’ ta hanyar rubuta ‘Congratulations’ a ƙarƙashin wannan hoton, zan ba da kyautan kati … ga mutane 50”.

Sai dai ba ta faɗi yawan katin da zata rabar ba a matsayin tukwicin ba.

Haka kuma amaryar ta Lilin Baba ba ta bayyana adadin yawan lokacin da ta kwashe tana ɗauke da juna biyun ba.

An taya ta murna sosai

Mutane da dama masu bibiyar ta a Instagram sun taya ta murna tare da yi mata fatan alheri.

Idan ba a manta ba dai anyi bikin Ummi Rahab da Lilin Baba a ranar Asabar, 18 ga watan Yuni, 2022, a Tudun Murtala, Kano, a kan sadaki N200,000.

Waliyyin ango jarumi Ali Nuhu, shine ya amsarwa Lilin Baba auren Ummi Rahab.

Dalilin da ya hana Adam Zango zuwa ɗaurin auren Ummi Rahab

Kamar yadda Tashar Tsakar Gida ta nuna, manya-manya jarumai sun samu damar halartar daurin auren Lilin Baba da Ummi Rahab, amma banda Adam A. Zango.

Ali Nuhu shi ne wakilin ango inda ya amsar masa auren amaryarsa kuma bidiyon wurin daurin auren ya tabbatar da hakan.

Manyan jarumai maza sun yi nasarar zuwa wurin daurin auren inda su ka yi wa jaruman kara tun daga Ali Nuhu, Umar M Sherif, TY Shaban da sauran

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe