27.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Bana jin ɗaɗin abinda rahama Sadau take yi – inji wata matashiya

LabaraiKannywoodBana jin ɗaɗin abinda rahama Sadau take yi - inji wata matashiya

Wata matashiya mai suna Maryamah ta bayyana cewa gaba ɗaya bata jin daɗin abinda jaruma Rahama Sadau take yi na yanda take shiga ta bayyana surar jikin ta.

Tana mutunta Rahama Sadau

Ta bayyana hakan ne a wani rubutu da tayi a shafin ta na Tuwita, inda ta nuna cewa ita bata jin daɗin yadda Rahama Sadau ɗin ke yin shigar ta saboda tana matuƙar mutunta ta.

Ta ƙara da cewar matan dake yin ƙoƙari wajen bin dokokin Allah suna matan da suka fi kyawu a cikin wannan duniyar.

“Matan da suke yin ƙoƙari wajen bin hanyar Allah suna suka fi kyawu a duniyar nan. Bana jin daɗin abinda kike yi saboda kina da daraja sosai a gurina.” inji ta.

Mace bata buƙatar yin abinda zata ɗau hankalin maza

Ta kuma ƙara da cewar addinin Islama yana bawa mace kwarjini da ƙarfi ta yadda bata da buƙatar ta riƙa ƙoƙarin yin abinda za’a kalleta ko kuma buƙatar janyo hankalin mutane zuwa gare ta kamar yadda sauran mutane keyi.

Sai dai kuma wasu suna ganin tayi daidai wajen baiwa Rahama Sadau wannan shawara a yayin da wasu kuma suke ganin sigar da tabi wajen bada shawarar bata yi ba.

Bai dace a bawa jarumar shawara cikin mutane ba

Wani mai amfani da kafar ta tuwita mai suna Abdulsalam Bashir Dungus ya nusar da matashiyar kan cewa bai dace ta fito cikin mutane tana baiwa jarumar shawara ba. Kamata yayi ta bita a asirce ta bata shawarar, a cewar shi.

Sai dai ana ta ɓangaren, matashiyar ta nuna cewa wannan shine abinda zata iya yi tunda ita ba zata iya haɗuwa da jarumar ba.

A wani labarin na daban kuma, kunji labarin yadda wata mata da ‘ya ‘yanta 8 sun ƙone ƙurmus a wata gobara

Wata mata, ‘yar asalin ƙasar Siriya tare da ‘ya ‘yanta su 8 sun ƙone ƙurmus a wata gobara da ta kama a gidan su dake arewa maso yammacin ƙasar Turkiyya.

Wata kafar yaɗa labarai ta ƙasar ta Turkiyya ce ta wallafa labarin inda tace yaran da suka mutu yawancin su ‘yan tsakankanin shekara ɗaya ne zuwa 11.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe