34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Kyau na yayi yawa, ban dace in yi aiki ba, kamata yayi in ci daga ɗangare, budurwa

LabaraiKyau na yayi yawa, ban dace in yi aiki ba, kamata yayi in ci daga ɗangare, budurwa

Wata fitacciyar budurwa ‘yar asalin kasar Canada ta janyo surutai bayan bayyana wa mutane cewa kyawunta ya yi yawa don hakan ba za ta iya aiki ba, Legit.ng ta ruwaito.

Zukekiyar budurwar ta ce bai dace ace kyakkyawar mace irinta ta dinga tashi tun 6 na safe don shiryawa saboda zuwa aiki ba.

Budurwar wacce ‘yar TikTok ce fitacciyat ta ce gaskiya bata dace da zuwa aiki ba.

Lucy Welcher ta saki bidiyo ne yayin da ta bayyana wannan ra’ayin akan kanta inda tace har karshen rayuwarta ba za ta iya wahalar aiki ba.

A cewarta:

Ba na don yin aiki har karshen rayuwata. Kuna ganin na dace da in dinga tashi tun karfe 6 na safe har nan da shekaru 60 masu zuwa?

Ina! Kyau na ya zarce hakan!”

Direban tasi ya sha kuka bayan budurwarsa ta auri wani daban a ɓoye

Wata budurwa ta karyawa wani direban tasi zuciyar sa bayan ta auri wani daban ba shi ba.

Direban na tasi ɗin dai sun kwshe shekara uku suna soyayya da budurwar amma ta auri wani ta kyale shi ba tare da sanin sa ba.

Direban ya sha matuƙar mamaki

Wata mai amfani da @cassy_collins_ a shafin Twitter ta bayar da wannan labarin inda ta bayyana cewa taga direban tasin yana sharɓar kuka bayan ta shiga motar sa. Jaridar Legit.ng ta rahoto.

A cewarta, direban ya gano cewa budurwar ta sa wacce yakai tashar mota ranar Talata 1 ga watan Nuwamban 2022, tayi aure kwanaki kaɗan a ranar Asabar 5 ga watan Nuwamban 2022. Sun dai kwashe shekara uku tare suna soyayya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe