24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Malam Alin Kwana Casa’in ya maka matashin da ya yaɗa hirar batsa da sunansa a kotu

LabaraiKannywoodMalam Alin Kwana Casa'in ya maka matashin da ya yaɗa hirar batsa da sunansa a kotu

Sahir Abdulaziz, wanda aka fi sani da Malam Ali na shirin Kwana Casa’in mai dogon zango ya bayyana yadda wani matashi ya yada mummunar hira inda yace shi ne yayi ta da wata budurwa yana neman lalata da ita.

A cewarsa matashin mai suna Aliyu Imam Indabawa ya nemi kudi ne a hannunsa shi kuma yaki ba shi, hakan ya hassala shi ya yanke shawarar bata masa suna.

Ya yana da rahoton kiran da matashin yayi masa har sau biyu inda ya nemi kudi a hannunsa. A cewarsa shi kuma yace ya dade be yada hirar ba, hakan yasa yake zargin ya yada.

Ya bayyana wa jami’an hukumar ‘yan sanda dalla-dalla akan yadda komai ya auku, inda yace yana bukatar a bi masa hakkinsa don an yi matukar bata masa suna.

A bidiyon wanda Aliyu Samba ya wallafa, an ji muryar Malam Ali ya ce ba ya irin wannan hirar da mutane kasancewar ya san an san shi, sannan ganin daukakar da Allah yayi masa ne yake zargin ya sanya matashin ke neman bata masa suna.

Ku ci gaba da bibiyar Labarun Hausa don jin yadda ta kaya.

Ya maka matashin a kotu

Bidiyon Malam Ali na Kwana Casa’in yana kutuntuma wa Rayya ashar a wurin daukar fim

Wani bidiyo da ya dinga yawo a kafafen sada zumuntar zamani ya bayyana Sahir Abdul, wanda aka fi sani da Malam Ali a cikin shirin Kwana Casa’in mai dogon zango yana kutuntuma wa Rayya, abokiyar sana’arsa ashar na cin mutunci, Tashar Tsakar Gida ta ruwaito.

Alamu na nuna cewa a wurin daukar fim din aka yi wannan rikicin don daga bidiyon za ka gane cewa a gidan Bawa Mai Kada aka dauki bidiyonsa yana zagin.

A cikin bidiyon an ji inda Malam Alin yake korafi yana cewa ya zo wurin daukar fim ba shi da lafiya amma babu wani cikinsu da ya tambaye shi ya jikinshi kuma ana cewa an kula da shi.

An ji yana auna zagi sosai har yake cewa idan an ga dama a cire shi daga aikin.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe