Wata budurwa ta karyawa wani direban tasi zuciyar sa bayan ta auri wani daban ba shi ba.
Direban na tasi ɗin dai sun kwshe shekara uku suna soyayya da budurwar amma ta auri wani ta kyale shi ba tare da sanin sa ba.
Direban ya sha matuƙar mamaki
Wata mai amfani da @cassy_collins_ a shafin Twitter ta bayar da wannan labarin inda ta bayyana cewa taga direban tasin yana sharɓar kuka bayan ta shiga motar sa. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
A cewarta, direban ya gano cewa budurwar ta sa wacce yakai tashar mota ranar Talata 1 ga watan Nuwamban 2022, tayi aure kwanaki kaɗan a ranar Asabar 5 ga watan Nuwamban 2022. Sun dai kwashe shekara uku tare suna soyayya.
Ta ƙara da cewa:
“Mutane ya kamata ku daina tarwatsa rayuwar wasu irin haka, zaluncin yayi yawa.”
Mutane sun tofa albarkacin bakin su
@TooshModels ta rubuta:
“Ta samu wani wanda ya shirya ne. Shiri a nan na nufin kuɗi. Direban tasin bai shirya ba, har yanzu fafutuka yake yi. Mata ba ruwan su.”
@Flotus_wendy ya rubuta:
“Abu ɗaya da nake alfahari da shi, shine duk irin rashin mutuncin da aka yi min ba zan taɓa yin hakan ga wani ba. Wannan doka ce.”
@Judriez ya rubuta:
“Wai irin waɗannan labaran dama na faruwa da gaske? Ta yaya zaka kasa ganewa cewa wanda kake tare da shi yana shirya wani babban abu kamar irin aure? Hakan na nufin dama can taren ku bata kai tare ba.”
@_greatdre ya rubuta:
“Ina tausayin mace ta gaba da zata ƙara shigowa cikin rayuwar sa.”
Budurwa ta fasa auran angonta ana saura kwana uku daurin aure, ta bayyana dalilan ta
Wata budurwa ta fasa auran mijin da zata aura ana saura kwana uku a daura musu aure.
Wata shahararriyar mai watsa labarai, Amanda Chisom, itace ta sanya hoton wallafar da budurwar tayi na cewa ta fasa auran.
A cikin rubutun da budurwar tayi a shafin Twitter, tace koda yaushe mijin da zata aura yana ce mata kudin sa na a asusun da ba a tabawa
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com