36.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Mata da ‘ya ‘yanta 8 sun ƙone ƙurmus a wata gobara

LabaraiMata da 'ya 'yanta 8 sun ƙone ƙurmus a wata gobara

Wata mata, ‘yar asalin ƙasar Siriya tare da ‘ya ‘yanta su 8 sun ƙone ƙurmus a wata gobara da ta kama a gidan su dake arewa maso yammacin ƙasar Turkiyya.

Yawancin yaran basu wuce shekara 11 ba

PM News ta ruwaito wata kafar yaɗa labarai ta ƙasar ta Turkiyya da ta wallafa labarin inda tace yaran da suka mutu yawancin su ‘yan tsakankanin shekara ɗaya ne zuwa 11.

Gwamnan Bursa, wato inda lamarin ya faru, Yakup Canbolat ya bayyana cewa matar mai shekaru 31, tare da ‘ya ‘yanta su 6, da kuma ‘ya ‘yan ‘yar uwar ta su biyu sun ƙone ƙurmus ne a gidan su dake a Bursa da daren jiya Talata.

abun tafasa ruwa ne ya jawo gobarar

Canbolat yace binciken da aka gudanar ya gwada cewa akwai yiwuwar abin tafasa ruwa na wuta ne dake a hawa na biyu na gidan da matar da ‘ya ‘yan nata suke a zaune ne yayi sanadiyyar tashin wutar.

Ance kuma akwai wasu mutane uku waɗanda ke zaune akan hawan benan da ke sama da suka tsira da ‘yan raunuka, waɗanda sanadiyyar haka tasa aka kaisu asibiti.

Matar da ‘ya’yan nata suna gudun hijira ne

Ance matar da yaran nata suna gudun hijira ne sakamakon rikicin ƙasar Siriya da ya ƙi ci ya ƙi cinye wa.

A wani labarin na daban kuma, kunji cewa wani ango ya mutu bayan kwana 2 da daurin auren shi.

Wani ango da aka bayyana sunan shi da alhaji Kabiru Mai Magani Saminaka ya mutu bayan kwanaki biyu da ɗaura auren sa akan hanyar sa ta dawowa Saminaka.

Angon ya mutu ne a sakamakon mummunan haɗarin mota da faru dashi a yayin da yake komawa gida Saminaka, ƙaramar hukumar Lere jihar Kaduna daga Pambeguwa, a jihar ta Kaduna, a ranar Litinin ɗin da ta gabata.

Labarin mutuwar wannan sabon ango dai ya yaɗu cikin ƙanƙanin lokaci a kafafen sada zumunta na zamani musamman ma dai a kafar Facebook inda ‘yan uwa da abokan arziƙin mamacin suka dinga rubuta alhinin su da kuma addu’o’i.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe