27.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

An kai wa tawagar motocin Atiku Abubakar mummunan hari a Maiduguri

LabaraiAn kai wa tawagar motocin Atiku Abubakar mummunan hari a Maiduguri

An farmaki tawagar motocin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na jami’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), a birnin Maiduguri, jihar Borno a ranar Laraba.

An ji ƙarar harbe-harbe

A wani bidiyo da aka gani a kafafen sada zumunta, an ga wasu mutane sun ranta ana kare yayin da harbe-harbe suka bazu a saman iska. Jaridar Daily Trust ta rahoto.

Tawagar yaƙin neman zaɓen jam’iyyar adawa ta PDP ta dira jihar Borno, wacce take a ƙarƙashin ikon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), a ranar Laraba.

An lalata wasu daga cikin motocin tawagar Atiku Abubakar

Wakilin jaridar Daily Trust yayi ido huɗu da motocin tawagar Atiku da aka lalata a filin taro na Ramat Square a Maiduguri, babban birnin jihar.

PDP ta ɗora alhakin kai harin kan APC

Kakakin yaƙin neman zaɓen Atiku Abubakar, Sanata Dino Melaye, ya ɗora alhakin kai harin akan jam’iyya mai mulki a jihar Borno.

Melaye ya koka da cewa sama da mutum 70 suka jikkata.

“Suna son su hana mu yin yaƙin neman zaɓen ne, a yanzu da nake magana, mutum 74 sun jikkata suna asibiti.”

“Ƴan daban APC sun lalata motoci da dama.” Inji shi

Har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton, jam’iyyar APC ba tave komai ba dangane da zargin da Dino Melaye yayi.

Wakilin jaridar Daily Trust ya ga dubunnan mutanen da aka zargin. ƴan daban siyasa ne a sassa daban-daban na kan titin hanyar Maiduguri/Kano.

Ƴan bindiga sun farmaki tawagar ɗan takarar gwamnan APC a Kaduna, sun sace jiga-jigan jam’iyyar

A wani labarin na daban kuma, ƴan bindiga sun kai farmaki kan tawagar ɗan takarar gwamnan APC a Ƙaduna, inda suka yi awon gaba da wasu jiga-jigan jam’iyyar.

Ƴan bindiga sun sace wasu ƙusoshin jam’iyyar APC a jihar Kaduna a wani harin da ya auku akan hanyar Kaduna-Kachia a jihar Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa harin ya auku ne a wani waje da ake kira Tashar Icce wanda yake kusa da ƙauyen Kujama a ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe