Domin nuna goyon bayan su mata ƴan ƙasar Iran masu zanga-zangar ƙin jinin hijabi, kusan aƙalla mata miliyan 50 sun ƙona hijaban su a ƙasar Indiya.
Lamarin ya auku ne a gaban babban ɗakin taro na Kozhikode a ƙasar Indiya, matan sun kuma rera waƙokin nuna goyon bayan su ga ƴan ƙasar ta Iran masu zanga-zangar. Jaridar The Islamic Information ta rahoto.
Lamarin shine na farko da ya auku a Indiya
Wannan shine karon farko da mata a Indiya suka fito domin nuna goyon bayan su ga masu zanga-zangar na ƙasar Iran.
Da misalin ƙarfe 6 na yamma, an ƙona hijabai bayan wani taro da ƙungiyar ‘Islamic Free Thinkers Association’ ta shirya a babban ɗakin taro na Kozhikode.
An zargi jami’an tsaro da halaka mutane da dama
Ɗaruruwan mutane ne dai jami’an tsaron Iran suka halaka domin murƙushe zanga-zangar da ta ɓarke bayan kisan Mahsa Amini mai shekara 22 a duniya, wacce ta rasu yayin da take garƙame a hannun ƴan sandan gyaran tarbiƴƴa bisa sanya hijabi ba yadda ya dace ba.
Zanga-zanga ta ɓarke bayan rasuwarta, inda mata ta dama suka fito tituna domin nuna ɓacin ran su.
Haka ma a sassa daban-daban na duniya mata da dama ciki har da ƴan makaranta sun gudanar da zanga-zanga inda suka ƙona hijaban su domin nuna goyon bayan su ga matan ƙasar Iran.
Mata da dama a sassa daban-daban na duniya sun aske gashin kan su domin nuna goyon baya. A dalilin rasuwar Mahsa Amini, zanga-zanga ta ɓarke a wurare da dama a ƙasar Iran.
Masha Allah: Fatima Payman, musulma mai Hijabi ta farko da aka zaba a matsayin Sanata a kasar Australia
Mace ta farko da ke sanya Hijabi ta ja hankalin jama’a bayan ganin ta lashe zabe a matsayin ‘yar majalisar dattawa a yammacin Australia ranar 20 ga watan Yuni, wanda hakan yasa ta kafa tarihin zama sanata ta farko mai sanya Hijabi a gabadaya tarihin kasar Australia kuma sanata mai mafi karancin shekaru.
Sunanta Fatima Payman, shekarunta 27 kuma asali ‘yar gudun hijira ce wacce ta baro Afghanistan zuwa Australia lokacin tana da shekaru 8 da haihuwa.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com