34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Ango ya mutu bayan kwana 2 da daurin auren shi

LabaraiAngo ya mutu bayan kwana 2 da daurin auren shi

Wani ango da aka bayyana sunan shi da alhaji Kabiru Mai Magani Saminaka ya mutu bayan kwanaki biyu da ɗaura auren sa akan hanyar sa ta dawowa Saminaka.

Angon ya mutu sakamakon haɗarin mota

Angon ya mutu ne a sakamakon mummunan haɗarin mota da faru dashi a yayin da yake komawa gida Saminaka, ƙaramar hukumar Lere jihar Kaduna daga Pambeguwa, a jihar ta Kaduna, a ranar Litinin ɗin da ta gabata.

Labarin mutuwar wannan sabon ango dai ya yaɗu cikin ƙanƙanin lokaci a kafafen sada zumunta na zamani musamman ma dai a kafar Facebook inda ‘yan uwa da abokan arziƙin mamacin suka dinga rubuta alhinin su da kuma addu’o’i.

Yaje ta’aziyyar mutuwa ne shima

Ance shima yaje wata gaisuwa ce ta mutuwa da aka yi a garin Pambeguwa dake jihar ta Kaduna a yayin da wannan haɗarin ya same shi kan hanyar komawa.

Wani mai suna Jamilu Suleiman Saminaka ya wallafa labarin mutuwar a shafin shi na Facebook inda ya bayyana cewa kwana biyu kenan da ƙara auren Alhaji Kabiru Saminaka. Ya bayyana cewa ya mutu ne akan hanyar sa ta dawowa daga wajen wata ta’aziyya da yaje Pambeguwa.

Kwanan shi biyu kenan da ƙara aure

“Innalillai wa’inna ilaihi raji’un. Bayan kwana biyu da karin Aurenshi Allah ya karbi rayuwarsa a hanyarsa tazuwa ta’aziya Garin Pambegua.

Allah yajikan Alh Kabiru bilhakki
Mai magani, ya karbi shahadarsa Alfarman Manzon Allah S. A. W. Mukuma idan tamu tazo Allah yasa mucika da Imani ” inji Jamilu Sulaiman.

Mutane da dama sunyi tsokaci na jimami gami da addu’o’i dangane da mutuwar wannan ango a hatsarin mota. Sun wallafa hotunan shagulgulan bikin wanda ba’a daɗe da yin shi ba.

FB IMG 1667964392730
FB IMG 1667964388961

Wani ma mai suna Abdullahi Usman Saminaka ya wallafa labarin gami da wallafa wani hoto na daga hotunan shagalin bikin, tare da yima mamacin addu’a.

“Inna-Lillahi-wa-Inna-Ilaihirraji’un
Allah yayima Alhaji Kabiru mai magani Rasuwa. Allah yaji kanshi yasa ya huta ameen.”

“Innalillai wa’inna ilaihi raji’un. Bayan kwana biyu da karin Aurenshi Allah ya karbi rayuwarsa a hanyarsa tazuwa ta’aziya Garin Pambegua.

Allah yajikan Alh Kabiru Mai magani, ya karbi shahadarsa Alfarman Manzon Allah S. A. W. Mukuma idan tamu tazo Allah yasa mucika da Imani.” inji wani Haruna Nuhu Saminaka.

A wani labarin na daban kuma, kunji cewa Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa wato EFCC, Abdulrashid Bawa, yayi magana kan hukuncin kotu na tura shi zuwa gidan gyaran hali.

Wata babbar kotu a birnin tarayya Abuja mai zamanta a Maitama ta yankewa Abdulrashid Bawa hukunci bisa raina kotu.

Kotun ta umurci hukumar EFCC da ta mayarwa wani tsohon darekta a hukumar sojin sama, Air Vice Marshal (AVM) Rufus Adeniyi Ojuawo, motar sa ƙirar Range Rover, da Naira miliyan 40 (N40m).

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe