Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa wato EFCC, Abdulrashid Bawa, yayi magana kan hukuncin kotu na tura shi zuwa gidan gyaran hali.
Wata babbar kotu a birnin tarayya Abuja mai zamanta a Maitama ta yankewa Abdulrashid Bawa hukunci bisa raina kotu.
Kotun ta umurci hukumar EFCC da ta mayarwa wani tsohon darekta a hukumar sojin sama, Air Vice Marshal (AVM) Rufus Adeniyi Ojuawo, motar sa ƙirar Range Rover, da Naira miliyan 40 (N40m).
Hukumar EFCC ta ƙi bin umurnin kotu da gangan
Sai dai, hukumar ta ƙi bin wannan umurnin na kotun.
A dalilin haka, sai alƙalin kotun ya ya tura Abdulrashid Bawa zuwa gidan gyaran hali na Kuje bisa ƙin bin umurnin kotun da gangan.
Da yake magana dangane da hukuncin na kotun a wata hira da jaridar Daily Trust, shugaban na EFCC yace tuni ya ɗaukaka ƙara.
Shugaban na EFCC ya ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotun
Shugaban na EFCC wanda ya bayyana a gaban kwamitin yaƙi da cin hanci na majalisar wakilai ta tarayya a ranar Talata, domin kare kasafin kuɗin hukumar sa, yace a bar doka tayi aikin ta.
“Eh, mun ɗaukaka ƙara akan hukuncin, saboda haka zamu bari doka tayi aikin ta yadda ya dace.” Inji shi
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta kama wani dan kasar China bisa laifin hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba
A wani labarun na daban kuma, hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta cafke wani ɗan ƙasar Chana bisa laifin haƙo ma’adanai ba kan ƙa’ida ba
Hukumar yaki da cin hanci shiyyar garin Ilorin, EFCC, ta kama wani dan kasar China mai suna Gang Deng.
Gang dan kimanin 29 da haihuwa, an kama sa ne bisa zargin hako ma’adanai ba bisa ka’ida ba a Ilorin, jihar Kwara.
An kama Mista Deng ne a ranar Juma’a, 9 ga watan Satumba, inda aka same shi da mallakar danyen ma’adinai ba tare da izini ba.
An kama mota dauke da ma’adanai da ake zargin lepidolite ne.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com