27.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Wata budurwa ta jawo cece-kuce bayan ta roƙi kada Allah ya bata haihuwa

LabaraiWata budurwa ta jawo cece-kuce bayan ta roƙi kada Allah ya bata haihuwa

Wata budurwa ƴar Najeriya ta bayyana cewa bata ganin cewa nan gaba zata haifi yara saboda ita gabaɗaya bata son yara.

A cewar ta, tana matuƙar jin mamaki duk lokacin da taji mata na nuna irin ƙaunar da suke wa yaran su. Jaridar Legit.ng ta rahoto.

Budurwar tace Allah bai haɗa jinin ta da na yara ba

Budurwar tayi nuni da cewa yara wahala ne kawai a gare ta sannan za ta tabbattar cewa kafin tayi aure ta sanar mijinta matsayar ta dangane da haifar yara.

A kalamanta:

“Kun san yadda ƴanmata da yawa suke son su zama iyaye su haifi yara kamar 15. Ni bana jin son yara. Ina jin cewa kawai yara wasu ƙarin wahala ne. Wani ƙarin ciwon kai ne. Ni bana tunanin zan taɓa haihuwar yara. Ba na son yara ko ɗaya.”

“Kafin na yi aure, zan gayawa mijina cewa ni sam bana son yara ko kaɗan. Ba yadda ya za a yi na haihu. Ni kawai bana son yara.”

Kalli bidiyon a nan

Mutane sun tofa albarkacin bakin su

@namama.1 ya rubuta:

“Ba kiyi laifin komai ba ƴar’uwa, na yi fatan cewa iyayen ki sun san hakan kafin su haife ki. Da basu haifa Jaka mummuna mace irin kiba.”

@for.hanadra ya rubuta:

“Babu komai don kin bayyana ra’ayun ku, amma yakamata ace kin bar hakan a zuciyar ki tunda baki san inda ze ƙare ba ko yadda za a fassara ba.”

@hikmagil ya rubuta:

“Mutane masu cewa Insha Allah ba zaki haifi ko ɗaya ba, kada ku manta yayin da kuke addua ga wani, kuma ana yi muku makamanciyar ta.”

@eyshaluv1 ta rubuta:

“Subhanallah ina son yara Allah ka albarkaceni da yara. Don Allah ku sanya ni a addu’a ina son yara shekara ta 6 da aure yanzu.”

@khadijaluv ta rubuta:

“Ina tunanin na fahimce ki, shekarun ki ne kawai suke magana, zan so jin haƙiƙanin yadda zaki ji shekara uku kacal bayan auren ki.”

Cike da izgili, budurwa ta wallafa hoton takalmin talakan da yaje gidansu neman aurenta

Wata budurwa ta yi wallafa wacce tayi matukar daukar hankalin jama’a yayin da wani yaje har gidan iyayenta yana neman aurenta.

Sai dai da alamu sam bai kayatar da ita ba don ta dauki hoton takalminsa wanda yayi yaga-yaga.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe