24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Baturiyar da ta fara sana’ar gwanjo da N2,000, ta tara N48m ta siya katafaren gida

LabaraiBaturiyar da ta fara sana’ar gwanjo da N2,000, ta tara N48m ta siya katafaren gida

Olivia Hillier ta fara sana’arta da $5 wato N2,000 da wata rigar da ta gani a shagon siyar da gwanjo, Legit.ng ta ruwaito.

Ita din daliba ce a Jami’ar da ke Michigan, Oakland inda ta fara siyar da wasu kayan gwanjo bayan ta siyo su a Poshmark, wata manhajar siyar da suttura.

Daga nan ta kara dagewa. Yayin da aka fara annobar COVID-19 a shekarar 2020, Hillier ta kula da cewa masu sana’a a Poshmark su na samun kudade masu yawan Gaskya ta hanyar siyar da nagartattun sutturu.

Wannan yasa tayi amfani da kudin riga daya wacce ta siyo a N2,000 ta siyar da ita a N8,000 ta kara saro wasu kayan.

Daga nan ne Ubangiji ya sanya wa Hillier hannu har ta kai ga samun N48.5 miliyan har da wata N35.2 miliyan ta shekarar da ta gabata.

A ko wanne wata yanzu haka, taba samun N2.5 zuwa 2.9 miliyan na riba kamar yadda CNBC ta bayyana.

Sannan da sana’ar ta siya katafaren gida mai dakunan biyar babu jimawa. A cewarta ta ki amsar bashin ko sisi don yanzu haka ribar ce tsagwagwa take samu.

Ta ce ta gano cewa yawancin masu siyar da gwanjo a shekarar 2020 ba kayansu bane, kawai su na wallafa hotuna ne daga wurin asalin masu siyarwa, idan an samu masu bukata sai su siyo su dora riba, a cewarta da haka ta fara.

Kuma ta ce yawancin masu siyan kayanta mata ne masu shekaru 25 zuwa 40.

Dan Najeriya yayi wuff da wata kyakkyawar baturiya, bidiyon yadda take masa hidima ya dauki hankula

Wani matashi dan Najeriya mai amfani da @kanorsamuel223 a manjajar TikTok ya saka wani bidiyon budurwar sa Baturiya a kafar.

Wani bangare na daga cikin bidiyon ya nuna kyakkyawar baturiyar na amfani da tukunyar gas tana soya masa filanten. Ta nuna cewa lallai ita fa taga wurin zama.

Matashin ya samu kyakkyawar baturiya

Idan da ba domin yanayin kalar fatar jikinta ba, da sai ayi tunanin cewa ‘yar Najeriya ce bisa yadda take gudanar da dafa abincin.

Mutane da dama sun yi tururuwa zuwa bangaren yin sharhi domin tambayar matashin yadda akayi ya samu wannan kyakkyawar baturiyar a matsayin budurwar sa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana raayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe