27.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Ubangiji ba ya son kyautar rainin wayau, Fasto ya raina N30 da aka ba shi sadaka

LabaraiUbangiji ba ya son kyautar rainin wayau, Fasto ya raina N30 da aka ba shi sadaka

Wani fasto ya isa daidai tashar motoci inda ya dinga yi wa matafiyi wa’azi mai ratsa jiki akan muhimmancin bayar da sadaka, LIB ta ruwaito.

Anan ne wani fasinja ya dauki N30 ya ba shi, wanda ran faston yayi matukar baci. Yayin da ya ki amsar kudin, ya zargi fasinjan da raina Ubangiji inda yayi masa wankin babban bargo.

Ya tambayi fasinjan dalilin da yasa bai yi amfani da N30 din wurin siyan na’urar salula ba.

Ya kara da cewa shi ba ya kin amsar sadaka, amma Ubangiji ya tsani sadakar rainin wayau.

Lamarin ya bai wa mutane da mamaki kasancewa kowa ya san cewa sadaka ba ta kadan kuma ba ta yawa. \

Sai dai a wurin wannan faston, ya bukaci mutumin ya bayar da kudi mai kauri in har yana so ya samu cikakken lada.

Ga bidiyon:

Yadda wani babban fasto yayi wa wata matar aure fyade yayin yi mata addu’ar tsarkakewa

Wani babban fasto a wata coci a Rumuaholu a karamar hukumar Obio/Akpor, ta jihar Ribas, yayi wa wata matar aure fyade yayin yi mata addu’ar samun tsarkaka.

Wani mamba na wata kungiyar masu rajin kare hakkin bil’adama ta ‘Center for Basic Rights and Accountability Campaign’, Prince Wiro, shine ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin 10 ga watan Oktoban 2022. Jaridar Legit.ng ta rahoto.

Yadda faston yayi wa matar auren fyade

Wiro ya bayyana cewa faston yayi wa matar ta karfi bayan ya nemi mahaifiyarta da ta dan basu waje lokacin da ake addu’ar, sannan an tsare shi a ofishin ‘yan sanda na Ozuoba.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe