Kotu ta bayar da umurnin a bulale wasu masu barkwanci a TikTok a Kano, Mubarak Muhammad da Nazifi Muhammad, bisa zargin ɓata sunan gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje.
Kotun ta bayar da wannan umurnin ne a ranar Litinin 7 ga watan Nuwamban 2022, bayan taurarin na TikTok sun zargi Ganduje da cin hanci. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
An cafke ƴan TikTok ɗin bayan sun ci mutuncin Ganduje
An dai cafke masu barkwancin ne sannan aka tura su zuwa kotu bayan wani bidiyon su na TikTok ya bayyana inda suke zargin Ganduje da cin hanci.
An tura su kotun ne bisa tuhumomi guda biyu na ɓata suna da tada fitintinu .
A wajen ƙarar, alƙalin kotun, Aminu Gabari, ya bayar da umurnin a yiwa kowane daga cikin su bulala 20 sannan kuma ya sanya su sharar harabar kotun har na tsawon kwana 30.
Kotun ta kuma umurci masu barkwancin na TikTok da kowanen su biya tarar N10,000.
Ana kammala yanke hukuncin, wani ma’aikacin kotun ya ɗauko bulala ya yiwa kowanen su guda ashirin.
An dai bulale su ne a bainar jama’a ciki har da wasu ƴan TikTok ɗin da suka zo kotun domin nuna musu goyon baya.
Ana fatan hukuncin ya zama darasi ga sauran mutane
Alƙalin yace yana fatan cewa hukuncin zai zama izna ga saura waɗanda ke amfani da kafafen sada zumunta sannan ya tabbatar cewa sun yi takatsantsan da kuma girmama manya.
Lauyan gwamnatin jihar, Wada Wada, yace ya gamsu da hukuncin inda ya ƙara da cewa yana fatan abinda ya faru ga ƴan TikTok ɗin ya zama darasi ga sauran mutane.
Tabarar da mata masu yabon ma’aiki ke yi ta zarce ta masu rawar TikTok da ‘yan fim, Fantimoti
Fitacciyar mawakiyar finafinai a baya, yanzu haka kuma sha’ira a fannin yabon manzon Allah SAW, Maryam Fantimoti ta ce tabarar da mata sha’irai masu yabon ma’aiki su ke yi, ta fi ta ‘yan rawar TikTok da ‘yan fim.
Kamar yadda ta shaida wa Freedom Radio Kano, ta ce dangane da shigarsu ta fitar da surarsu, cakudewa tsakanin maza da mata da suke yi ya munana.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com