24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Wata matashiya ta zama makauniyar lauya baƙar fata ta farko a Birtaniya

LabaraiWata matashiya ta zama makauniyar lauya baƙar fata ta farko a Birtaniya

Wata matashiyar budurwa ta zama makauniyar lauya baƙar fata ta farko a ƙasar Birtaniya. A wata gagarumar nasara wacce ta zama abin kwatance.

Matashiyar mai suna Jessikah Inaba, mai shekara 23 a duniya ta cancanci zama lauya a satin da ya gabata bayan ta shafe shekara biyar tana karatu a wata jami’a a birnin Landan. Kamar yadda majiyarmu ta rahoto.

Tayi amfani da wani abin koyon karatu na musamman

Ta kammala gabaɗaya karatunta ta hanyar yin amfani da allon makafi, sannan ta yabawa ƙawayenta da malamanta wajen taimaka mata wajen cike guraben.

Jessikah ba ta gani gabaɗaya hakan ya sanya sai dai tayi amfani da allon makafi a gabaɗaya zaman da tayi a jami’ar koyon aikin lauya ta Bloomsbury a birnin Landan.

Ta fara faratun karatun digiri a fannin lauya a shekarar 2017 kafin ta fara karatun digirin digir shekara biyu baya.

Dangane da nasarar da ta samu, Jessikah ta gayawa jaridar Mirror UK cewa:

“Wannan abin mamaki ne. Har yanzu na kasa yarda cewa nayi hakan. Watarana zan farka na ga yadda wannan abin ban mamakin yake.”

Ta sha matuƙar wahala sosai

“Na sha matuƙar wahala sannan har na fara tunanin na haƙura kawai, amma ƴan’uwana suka ƙara min ƙarfin guiwa.”

“Na yarda da kai na tun da farko, ba wani abu dangane da ni wanda yake nufin cewa ba zan iya samun wannan nasarar ba.”

“Na san cewa zan iya wannan aikin yadda yakamata, sannan yawan mutane iri na da za su koyi karatu ta wannan hanyar, yawan yadda zai ƙara sauƙaƙa.”

Ta ƙara da cewa jami’ar ta taimaka mata wajen shirya mata karatu na kai tsaye da mai koyarwa lokacin da matsalar littattafai ta so ta kawo mata cikas.

Daga yin shiga irin ta musulmai kawai sai maza musulmai suke ta turo min sako wai zasu aureni – Inji wata matashiyar kirista

Wata matashiya, ta bayyana  yadda maza musulmai suka dinga tururuwar sakonni gareta, a shafin ta na tuwita,  suna neman ta yarda ta zama mata a garesu. 

Kamar yadda yawancin mutane suka sani, yana da sauƙi a gane addinin mutane ta yadda suke sanya tufafi

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe