24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Matashin attajiri ya talauce bayan shirya biki na kece raini, an bar shi da tarin basussuka

LabaraiMatashin attajiri ya talauce bayan shirya biki na kece raini, an bar shi da tarin basussuka

Wani matashi ɗan Najeriya ya bayyana wani babban kuskure da ya tafka a rayuwar sa.

Matashin wanda magidanci ne wanda yace yana samun miliyoyin kuɗi a wata, ya bayyana cewa yayi kuskuren ɗaukar kuɗin kasuwancin sa domin yin biki na kece raini.

A cewar sa, kasuwancin sa na ta haɓaka, wanda har ya sanya an kai matakin da abokan sa suka zuba kuɗin su a ciki. Jatidar Legit.ng ta rahoto.

Ya tafka aikin dana sani

Sai dai abin takaici, bayan sun zuba kuɗaɗen su, sai kasuwancin ya fara ja da baya sannan gashi ya sanya ranar auren sa.

A maimakon ya biya mutanen dake bin sa bashi kuɗaɗen su, sai ya haƙiƙance cewa lallai sai ya shirya biki na kece raini, inda yake tunanin cewa zai mayar da kuɗin sa bayan an gama biki.

Sai dai hakan bai faru ba domin tun daga nan duniya tayi masa atishawar tsaki, inda ya talauce ga kuma ɗumbin basussukan da aka biyo shi.

Ga bidiyon nan ƙasa:

Mutane sun tofa albarkacin bakin su

Enabelokoye ya rubuta:

“Ina duba waje sharhi na ga mutane d dama na cewa ba gaskiya bane. Kada ku tsaya tunanin cewa wai sai mutane sun yi shiga mai kyau kafin ku yarda sun samu arziƙi. Ɓan taɓa ganin Elon Musk ya sanya kayan da suka wuce ƴar ƙaramar riga ko kwat ba. Mutanen mu yakamata su daina danganta kuɗin mutane da kayan da suka sanya.”

Emillee238 ya rubuta:

“Ya za ai mutumin da yake samun $10,000 ya kasance haka? lol wannan wanda yayi kama da mutumin da bai taɓa jin ƙamshin kuɗi ba a rayuwar sa.”

Nicebobby101 ya rubuta:

“Amma wannan bai yi kama da wanda ya samu wannan kuɗin ba. Kuɗi ba sa ƙarya duk kuwa da yadda kake son ka ɓoƴe su. Wannan gaskiya ce ba zagi bane.”

Mutane suna yaba kyawuna, amma duk da haka na kasa samun saurayi – matashiya

Wata matashiya mai tashe a soshiyal midiya ta koka kan yadda ta gaza samun tsayayyen saurayi duk da tarin mabiya da take da su a shafukanta na sada zumunta na zamani

Matashiyar mai amfani da suna Ms PuiYi a shafukan sada zumunta ‘yar shekara 24 ta koka kan yadda mutane da dama ke yabawa da irin kyawun da take dashi, amma kuma bata da tsayayyen saurayin da zata yi tarayya dashi a rayuwarta

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe