24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Magidanci ya cinnawa ƴaƴan matarsa wuta bayan ta ƙi yarda su yi kwanciyar aure

LabaraiMagidanci ya cinnawa ƴaƴan matarsa wuta bayan ta ƙi yarda su yi kwanciyar aure

Wani magidanci ya cinnawa ƴaƴan matar sa guda biyar wuta bayan ta hana shi su yi kwanciyar aure.

Magidancin mai suna Ojo Joseph mai shekara 54 a duniya ya aikata wannan aika-aikar ne a jihar Ondo.

Lamarin ya auku ne a unguwar Fagun cikin garin Ondo a ranar Lahadi 6 ga watan Oktoɓan 2022 da safe. Majiyar mu ta jaridar The Cable ta rahoto.

Yadda magidancin ya aikata wannan ɗanyen aikin

Joseph ya fusata ne inda ya cinnawa yaran wuta bayan mahaifiyar su ta ƙi yarda su yi kwanciyar aure.

Wanda ake zargin ya watsa man fetur a ɗakin da yaran ke yin barci sannan ya cinna masa wuta.

Ɗaya daga cikin yaran ya ƙone har lahira yayin da sauran suka samu munanan raunika inda ake duba lafiyar su a babban asibitin tarayya dake Owo.

Matar sa da tagwayen da suka haifa tare masu watanni sha takwas a duniya sun tsira daga wutar da ƴan ƙananan raunika.

Ƴan sanda sun tabbatar da aukuwar lamarin

Da take tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin hukumar ƴan sandan jihar, Funmi Odunlami, ta bayyana cewa tuni aka kama magidancin.

Ta kuma ƙara da cewa an fara gudanar da bincike sannan za a kammala kafin a tura wanda ake zargin zuwa kotu bisa zargin sa wuta da kisan kai.

Yadda magidanci ya lakadawa jaririn sa dukan tsiya saboda ya hana shi barci

A wani labarin na daban kuma, wani magidanci ya lakadawa jaririn sa shegen duka saboda ya hana shi ya samu barci mai daɗi.

Hukumar kare hakkin dan Adam ta kasa (NHRaC) da kungiyar mata ‘yan jarida (NAWOJ) reshen jihar Imo, sun yi kira ga gwamnatin jihar da hukumar ‘yan sanda da su gaggauta cafke tare da hukunta wani magidanci mai suna Mr Conidence Amatobi, bisa zargin lakadawa jaririn sa mai wata biyu a duniya shegen duka.

Mr Amatobi ya bugi jaririn mai suna Miracle da abin makale kaya na roba wanda yayi sanadiyyar karyewar hannun jaririn saboda ya hana shi ya samu barci mai dadi.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com


Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe