An kashe matashin ta hanyar soka mishi wuƙa
Wani matashi da aka bayyana sunan shi da Ashiru Nuhu Tofa ya rasa ranshi sakamakon soka mishi wuƙa da aka yi a yayin da yake dawowa daga hira da ya je wajen budurwar shi.
Wannan mummunan lamari dai ya faru ne jiya Asabar, 5 ga watan Nuwamba da daddare a garin Minna dake jihar Naija kusa da wani ofishin hukumar ‘yan sanda, kamar yadda labarin mutuwar matashin ya nuna.
‘Yan uwa da abokan arziƙi sun yi jimami
‘Yan uwa da abokan arziƙi na mamacin sun yi jimamin mutuwar matashin, inda suka wallafa hotunan shi a shafukan sada zumunta musamman ma na facebook don nuna alhininsu gami da addu’ar nema mishi gafara wajen Ubangiji.
Wani ɗan uwan mamacin mai suna Jamil Tofa ya wallafa labarin rasuwar mamacin, gami da bayyana lokaci da kuma gurin da za’a yi jana’izar matashin.
Tuni aka gudanar da jana’izar matashin a gidan mahaifinsa, Alhaji Nuhu tofa dake Limawa kan titin Katsina dake cikin garin Minna, kamar dai yadda ɗan uwan mamacin ya sanya a shafin shi na Facebook.
Ba’a gano ko su waye suka kashe shi ba
Har kawowa yanzu ba’a iya gani ko su waye suka kashe matashin ba ko kuma dalilin da yasa suka kashe shi ba. Sai dai wasu ma ganin hakan na da alaƙa da yadda masu aikata laifuka iri-iri ke ta ƙaruwa a garin na Minna.
Ana yawan samun makamanta irin wannan lamurran a birane da dama dake arewacin Najeriya. Ana alaƙanta hakan da ayyukan matasa masu ƙwacen waya ko kuɗaɗe a lokacin da dare yayi.
A wani labarin na daban kuma, wata fitacciyar jarumar wasan talabijin na musamman ‘yar ƙasar Faransa Marin El Himer, ta karɓi addinin musulunci inda kuma ta bayyana cewa waɗannan kwanaki da ta karɓi musulunci.
Kwana biyu bayan da ta karɓi addinin Musulunci, Eli Himer ta ɗora wasu hotuna nata a shafinta na Instagram sanye cikin hijabi a kusa da ɗakin ka’aba, guri mafi tsarki a musulunci.
Ta bayyana tsananin matuƙar farin cikin ta da wannan babban abu da ya sameta na karɓar addinin musulunci, domin tana fatan ta samu rayuwa mai kyau da zata ci gaba da yi mata jagora har ƙarshen rayuwar ta.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com