Wata fitacciyar jarumar wasan talabijin na musamman ‘yar ƙasar Faransa Marin El Himer, ta karɓi addinin musulunci inda kuma ta bayyana cewa waɗannan kwanaki da ta karɓi musulunci.
Ta ɗora hotunan ta a ɗakin ka’aba
Kwana biyu bayan da ta karɓi addinin Musulunci, Eli Himer ta ɗora wasu hotuna nata a shafinta na Instagram sanye cikin hijabi a kusa da ɗakin ka’aba, guri mafi tsarki a musulunci.
Ta bayyana tsananin matuƙar farin cikin ta da wannan babban abu da ya sameta na karɓar addinin musulunci, domin tana fatan ta samu rayuwa mai kyau da zata ci gaba da yi mata jagora har ƙarshen rayuwar ta, kamar yadda majiyar mu ta wallafa.
Tana fatan musulunci ya taimaki rayuwar ta
“In sha Allah, bani da wasu kalmomi isassu da za su iya bayyana irin tsananin murnar da zaƙuwa da nake a ciki a wannan yanayi. Tafiya ce wacce nake fatan zata ɗora ni akan madaidaiciyar hanya kuma ta taimaki rayuwa ta in Sha Allahu.
“Babu wasu isassun kalmomi da zan iya bayyana irin matuƙar farin cikin da nake ciki a wannan lokaci.” inji Eli Himer.
Ta ce wannan mataki da ta ɗauka na komawa musulunci tayi shi ne bisa tunanin ta da zuciyar ta da kanta.
Tana fitowa a shirin na musamman a Faransa
Jarumar dai ta kasance tana fitowa a cikin shirin talabijin na musamman na ƙasar Faransa mai taken ‘yarima da sarauniyar ƙauna’.
Masoya da magoya bayan ta ma bata mance da su ba inda sai da ta gode musu bisa kyautatawa da kuma goyan bayan da suka bayar.
Kamar yadda wata jaridar ƙasar Faransa ta wallafa, Himer ta girma ne a wajen ɗan uwan baban ta, ta ɗauki tsawon lokaci tana bincike akan inda ainihin baban nata yake. A cikin wannan binciken nata ne ta karɓi addinin musulunci.
A wani labarin na daban kuma, kunji yadda likitoci suka ciro ‘yan tayi guda 8 daga cikin wata jaririya.
Likitoci a Indiya sun yi nasar cire ‘yan tayi har guda takwas daga cikin wata jaririya mai kwana 21 biyo bayan ƙorafin da iyayen jaririyar suka kawo wajen likitoci.
Tun bayan da aka haifi jaririyar, iyayen ta sun lura da cewar tana fama da wani irin nau’i na kumburin ciki wanda da farko suka yi tunanin cewa ko ciwon sankara ne.
Sai dai bayan zuwan su asibiti, likitoci sun gudanar da aiki akan jaririyar inda suma a gwaje-gwajen da suka gudanar, sun yi tunanin cewa ko yarinyar na fama da ciwon sankara ne.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com