Gwamnatin tarayya ta maida martani kan ƙorafe-ƙorafen da malaman jami’a na ƙungiyar ASUU da kuma sauran al’umma suke yi dangane da batun rabin albashi da aka biya su na watan Oktoban da ya gabata.
Labaran da ake yaɗawa ba gaskiya bane
Wannan martani dai na zuwa ne daga ofishin ma’aikatar kula da ayyuka ta ƙasa biyo bayan labaran da ke yawo a kafafen sadarwa dangane da rabin albashin da aka biya malaman jami’o’i na ASUU na watan da ya gabata.
Ma’aikatar tace batun biyan rabin albashi da ‘yan ASUU suke ƙorafi akai ba gaskiya bane, iyaka dai an biya su kuɗaɗen kwanakin da suka yi aiki ne, kuma lissafa aka yi, kamar yadda Vanguard ta wallafa.
Albashin da aka biyan ‘yan ASUU a lissafe yake
A tattaunawar shi da ‘yan jarida, mai magana da yawun ma’aikatar, Olajide Oshundun, ya bayyana cewa labaran da ake ta yaɗawa ba gaskiya bane, kawai dai mutane suna yaɗa labaran da basu inganta ba.
Yace albashin da aka biya ‘yan ƙungiyar ta ASUU abu ne wanda aka yi shi a lissafe. Kuma anyi hakan ne saboda baza a iya biyan su kuɗin aikin da basu yi ba.
Bamu ce a biya su rabin albashi ba.
A cikin jawabin nashi, ya bayyana cewa ministan ayyuka na ƙasa wato Chris Ngige bai bawa ma’aikatar kuɗi umarnin biyan malaman jami’o’i na ASUU rabin albashi ba.
Jawabin ya kuma ƙara da cewar biyo bayan hukunci da kotu ta yanke, inda ta umarci ƙungiyar ASUU da ta janye yajin aiki da take yi, wanda kuma tura wakilan mu domin su tabbatar cewa malaman sun koma bakin aikin su.
“Ma’aikatar mu ta tura ma ma’aikatar kuɗi da tsare-tsare ta ƙasa saƙon cewa a biya malaman na jami’a albashin su. An lissafa daga randa suka koma aiki a Oktoba, wanda dashi ne aka ƙididdige aka biya su albashin su. Ba yadda za’a biya su kuɗin aikin da basu yi ba, kowa fa a takure yake.” inji Olajide.
Hakanan ma’aikatar kula da ayyukan ta yi martani ga shugaban ASUU na jami’ar Ɗanfodio dake Sokoto, Muhammad N. Al-Mustapha wanda ya zargi ministan da sanya son rai wajen nuna bambanci a wajen biyan wasu daga cikin ma’aikatan.
Ma’aikatar ta buƙaci al’umma da suyi watsi da duk wasu labarai da ake yaɗawa da ke nuni da cewa an nuna bambanci wajen biyan wasu daga cikin ma’aikatan.
A wani labarin na daban kuma, wata mata tace ba wani abu bane don mace ta ƙi yin aure.
Wata shahararriyar marubuciya mai suna Chimamanda Ngozi-Adichie, tace ita bata ga wani aibu ba, kan don mace taƙi yin aure ta zaɓi ta zauna ita kaɗai.
Tayi wannan kalamin ne a yayin da take gabatar da wata ƙasida a wajen wani taro a Legas wanda aka shirya kan rawar da mata ke takawa a ɓangarorin gudanarwa, kasuwanci da kuma sauran ayyukan al’umma.
Tace lokaci yayi da ya kamata mutane su daina takura ma mata akan batun ƙin yin auren su, inda tace suna da haƙƙin more yancin su yadda suke so.