LabaraiBa wani abu bane don mace ta ƙi yin...

Ba wani abu bane don mace ta ƙi yin aure – Marubuciya

-

- Advertisment -spot_img

Wata shahararriyar marubuciya mai suna Chimamanda Ngozi-Adichie, tace ita bata ga wani aibu ba, kan don mace taƙi yin aure ta zaɓi ta zauna ita kaɗai.

Tayi wannan kalamin ne a yayin da take gabatar da wata ƙasida a wajen wani taro a Legas wanda aka shirya kan rawar da mata ke takawa a ɓangarorin gudanarwa, kasuwanci da kuma sauran ayyukan al’umma.

Tace ya kamata a daina takura ma mata

Tace lokaci yayi da ya kamata mutane su daina takura ma mata akan batun ƙin yin auren su, inda tace suna da haƙƙin more yancin su yadda suke so, kamar yadda majiyar mu ta Punch ta wallafa.

Marubuciyar ta ƙara da cewa ba abu bane da ya kamata ace mutane suna damun mata da yawan tambayoyi akan yaushe ne zasu yi aure ko kuma waye zasu aura da makamantansu. Tace wannan yana sanya mata da yawan cikin damuwa.

“Na ga ‘yan mata da dama da suke damuwa kan rashin auren su. Zaka riƙa jin tambayoyi irinsu ‘tayi aure ne? Yaushe ne zata yi aure? Waye zata aura? Ina ganin abun yayi muni ace muna irin waɗannan maganganun. Hakan na sanya rayuwar ‘yan mata da yawa cikin damuwa.” inji Chimamanda.

Marubuciyar ta shawarci manyan mata

Marubuciyar ta kuma shawarci manyan matan akan kada su riƙa takura ma ‘yan mata kan batun rashin auren su. Tace suma ba wai basa don auren bane, sai dai ƙila basu samu wanda ya dace da su bane.

“Ina kira ga manyan yayanni, akan kada su riƙa takura ma ‘yan mata. Su ma da suna son samun farin ciki. Saboda haka don sun daɗe basu yi aure ba, hakan na nufin basu samu namijin da ya dace da su da zai basu farin ciki ba.” inji marubuciyar.

Suma suna son su samu farin ciki ne

Ta kuma ƙara da cewa bafa wani mummunan abu bane don mata sun zauna ba tare da yin aure ba. Kawai dai tana ganin cewa suna son samun farin ciki ne. Tace mata da dama da tayi magana da su akan haka sun gwada mata irin damuwar da suke shiga.

“Ba fa wani mummunan abu bane rashin auren ‘yan matan. Kawai dai suna son samun farin ciki ne. Damuwar tana yin yawa. Nayi magana da ‘yan mata da dama kan hakan, ba wai batu bane kan mace guda ɗaya, face kan mata da kuma irin gudummawar su a cikin al’umma.” inji Chimamanda.

Ta kuma ƙara da cewa bai kamata ana yanke ma mata hukunci ta hanyar duba da al’ada ba domin hakan zai iya daƙile su wajen fita a dama dasu a duniya don samun sauyi na gari.

A wani labarin na daban kuma, kunji yadda likitoci suka ciro ‘yan tayi guda 8 daga cikin wata jaririya.

Likitoci a Indiya sun yi nasar cire ‘yan tayi har guda takwas daga cikin wata jaririya mai kwana 21 biyo bayan ƙorafin da iyayen jaririyar suka kawo wajen likitoci.

Tun bayan da aka haifi jaririyar, iyayen ta sun lura da cewar tana fama da wani irin nau’i na kumburin ciki wanda da farko suka yi tunanin cewa ko ciwon sankara ne.

Sai dai bayan zuwan su asibiti, likitoci sun gudanar da aiki akan jaririyar inda suma a gwaje-gwajen da suka gudanar, sun yi tunanin cewa ko yarinyar na fama da ciwon sankara ne.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Latest news

Ɓeraye ne su ka bushe wiwin da mu ka ƙwace mai nauyin 200kg, ‘Yan sanda

‘Yan sandan Indiya sun koka kan yadda beraye su ka lamushe wiwi mai nauyin 200kg bayan sun kwace ta...

Daɗi miji: Bayan an kulle shi saboda ya laƙada mata duka, matar ta yi belin mijinta

Wata mata ta yi belin mijinta bayan an kama shi sannan a sakaya shi saboda ya lakada mata na...

Wata mata ta haihu a masallacin Annabi

Wata mata cikin masu gudanar da umra ta haihu a masallacin ma'aiki dake Madinah wacce ta samu taimakon wasu...

‘Yan gida daya su 11 sun mutu bayan cin wani abinci

Aƙalla mutane 11 ne 'yan gida ɗaya aka tabbatar da sun mutu bayan cin wani abinci da ake zargin...
- Advertisement -spot_imgspot_img

Matashi ya kaɗu bayan gano cewa budurwar sa a kango take rayuwa

Wata matashi ɗan Najeriya ya shiga kaɗuwa matuƙa bayan gano cewa budurwarsa ta tsawon wata takwas a cikin wani...

An zaɓi mace musulma ‘yar majalissar jiha a Amurka

Nabeela Syed, 'yar asalin ƙasar Indiya ta kasance mace musulma ta farko da aka zaɓa a matsayin 'yar majalissar...

Must read

Ɓeraye ne su ka bushe wiwin da mu ka ƙwace mai nauyin 200kg, ‘Yan sanda

‘Yan sandan Indiya sun koka kan yadda beraye su...

Daɗi miji: Bayan an kulle shi saboda ya laƙada mata duka, matar ta yi belin mijinta

Wata mata ta yi belin mijinta bayan an kama...
- Advertisement -spot_imgspot_img

You might also likeRELATED
Recommended to you