Likitoci a Indiya sun yi nasar cire ‘yan tayi har guda takwas daga cikin wata jaririya mai kwana 21 biyo bayan ƙorafin da iyayen jaririyar suka kawo wajen likitoci.
Cikin jaririyar ya kumbura
Tun bayan da aka haifi jaririyar, iyayen ta sun lura da cewar tana fama da wani irin nau’i na kumburin ciki wanda da farko suka yi tunanin cewa ko ciwon sankara ne, kamar yadda majiyar mu ta The Sun ta wallafa.
Sai dai bayan zuwan su asibiti, likitoci sun gudanar da aiki akan jaririyar inda suma a gwaje-gwajen da suka gudanar, sun yi tunanin cewa ko yarinyar na fama da ciwon sankara ne.
Jim kaɗan bayan kammala gwajin, an canza ma jaririyar asibiti zuwa wani asibiti na bincike da kula da cututtukan ƙananan yara dake birnin Ranchi na ƙasar ta indiya.
An gano abinda ke a cikin nata
Wasu likitocin bisa jagorancin wani ƙwararren likita mai suna dakta Mohammed Imran sun yi bincike inda suka gano cewa jaririyar na ɗauke da ‘ya ‘ya ‘yan tayi a cikin ta ne ba wai ciwon sankara ba kamar yadda ake hasashe.
Likitocin sun bayyana cewa ba’a cika samun irin wannan yanayin ba na samun wasu ‘ya ‘yan a cikin wani jaririn da ya kamata ace an haife su tare.
Likitoci sunyi nasarar cire ‘yan tayin
Bayan da likitocin suka gudanar da hoton cikin jaririyar, sakamakon da suka samu yayi matuƙar basu mamaki domin kuwa sun samu cewar akwai jarirai ‘yan tayi har su takwas a cikin wannan jaririya.
Likitocin sun aje jaririyar na tsawon kwanaki 21 ƙarƙashin kulawarsu kafin daga bisani suka gudanar da aikin ciro ‘yan tayin daga cikin ta.
Dakta Imran ya bayyana cewa aikin ya ɗauke su tsawon awa daya da rabi, kuma an yi shi cikin nasara.
A wani labarin na daban kuma, kunji yadda miji ya kashe matar shi saboda ta bincika mishi waya.
Wani miji ɗan kimanin shekara 37 ya kashe matar shi ta hanyar sarar ta da wuƙa a sassa daban-daban na jikin ta sakamakon binciken da ta yi mishi a cikin wayar shi ba tare da izinin shi ba.
Matar mai suna Mirriam Joni, yar shekara 27 dai bata wuce wata 3 da auran mijin nata ba. Majiyar mu tace ta ɗauki wayar shi sannan ta cire makullin dake kan fuskar wayar, inda daga bisani tayi mishi bincike, wanda a sanadiyyar hakan ne shi kuma ya kashe ta.
Jami’an ‘yan sanda sun tabbatar da faruwar mummunan lamarin wanda ya faru a ƙauyen Matsapa dake yankin Mutasa dake ƙasar Zimbabwe, inda suka bayyana cewa matar ta mutu a nan take.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com