Wata budurwa ta yi wallafa wacce tayi matukar daukar hankalin jama’a yayin da wani yaje har gidan iyayenta yana neman aurenta, yen.com.gh ta ruwaito.
Sai dai da alamu sam bai kayatar da ita ba don ta dauki hoton takalminsa wanda yayi yaga-yaga.
A bidiyon da ta wallafa a shafinta na Twitter mutane da dama sun ci dariya akan takalmin yayin da wasu su ka dinga caccakarta.
‘Yar Najeriyar mai suna @black.teenah ta saki bidiyon mai ban dariya na wanda yaje gidansu neman aurenta.
Da alamu matashi ne ya wanke kafa inda ya nufi a gaban iyayenta yana so su ba shi aurenta. Bayan ya cire takalman a bakin kofa ne Teenah ta dauki bidiyonsu.
Ta wallafa bidiyon takalminsa inda ta bayyana wa kawayenta cewa duk ya bi ya kosa yayi aure. Kamar yadda tasa bidiyon, ta kara da cewa:
“Kalli abinda wanda yazo neman aurena ya sanya. Anya ba wasa yake min ba,” Tace.
Da takalminsa muka gane shi, cewar ɗalibai bayan malaminsu yaje makaranta da Usaininsa
Wani matashi ya wallafa wani bidiyo akan yadda dan uwansa da su ke tagwaye ya kai masa ziyara a makarantar da yake aiki a matsayin malami, Legit.ng ta ruwaito.
Yayin da dan uwansan ya shiga aji, dalibai da dama sun yi mamaki inda su ka dinga kallonsu kasancewar kamar tasu har ta baci.
Yayin da wasu su ke ta wahala wurin bambanta su, nan da nan wasu daliban masu dabara su ka duba kafafunsu inda su ka gane malaminsu da takalminsa.
A wani bidiyo wanda shafin @twindiaries na TikTok su ka wallafa aka ga bidiyon wanda ya dauki hankalin mutane da dama.
Daliban sun yi matukar mamaki kasancewar ba su taba sanin cewa malaminsu tagwaye bane sai a ranar.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com