Masu bincike sun gano yadda nan kusa mutane za su sauya yanayin kirarsu saboda yawan amfani da abubuwan da fasahar zamani ta kawo, LIB ta ruwaito.
Za su koma wata siffa mai suna “Mindy” wacce wuyanta ya dara na mutane kauri, ga kusumbi sai kuma karamar kwakwalwa.
Siffar Mindy taba da ban tsoro kuma akwai yuwuwar mutane su koma haka nan gaba kadan bisa binciken Toll Free Forwarding. Kakakin yace:
“Fasaha ta sauya mana hanyoyin neman kudin. Mu na samun damar amfani da abubuwan da fasaha ta kawo har da wadanda ke iya shiga aljihunmu, ko kuma ince akwai damar yin sana’o’i ta wayar salula. Lallai fasaha ta kawo abubuwa da dama kuma babu alamar za a tsaya da gano sabbin abubuwa.
“Yayin da fasaha ke ta samar da ayyuka, cigaba da ilimomi, akwai kuma yadda take sauya kira da halittar dan Adam.”
Ya bayyana cewa dan Adam na da saurin amsar sauyi, hakan zai bayar da damar canjawarsa a hankali daga wata surar zuwa wata.
Ya ce masu amfanin da wayar salula da kwamfuta su na iya sauyawa a yanayin zaman su.
Musamman wurin kallon fuskar waya ko kwamfutar, wajibi ne mutum ya rakwafa. Ya ce yayin rike waya, idan mutum zai kula zai gane yadda ya ke kwalmada kafadarsa ko da kuwa wurin dannata ko amsa waya ne.
Sannan a hankali wuyan mutum yana kwalmadewa ba tare da ya kula ba.
Gwamnatin tarayya zata kara kashi 5% na haraji kan kiran wayan salula
Nan ba da dadewa ba ‘yan Najeriya za su fara biyan harajin kashi 12.5 na ayyukan sadarwa a daidai lokacin da gwamnatin tarayya ke shirin kara harajin kaso biyar wanda ya hada da ayyukan sadarwa a Najeriya.
Hukumar sadarwa ta shirya taro
Ministar kudi da tsare-tsare ta kasa, Zainab Ahmed ce ta bayyana haka a wani taron masu ruwa da tsaki kan aiwatar da haraji kan ayyukan sadarwa a Najeriya ranar Alhamis a Abuja.
Hukumar Sadarwa ta Najeriya NCC ce ta shirya taron.
Za a kara kashi 5% akan wanda ake biya a da
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa, za a kara biyar akan kashi 7.5 na haraji da ake biya a da wato VAT, kan ayyukan sadarwa.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com