A jiya juma’a ne dai aka daura auren jaruma Ruƙayya Dawayya da angon ta Isma’ila Na’abba Afakallahu, shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano a masallacin Tishama dake birnin Kano.
Mutane da dama ne suka halarci bikin
Mutane da dama daga ciki da wajen masana’antar Kannywood sun samu halartar ɗaurin auren na Ruƙayya Dawayya da kuma sauran shagulgula da suka biyo baya na cikar biki.
A cikin hotunan za’a iya ganin jaruman fim musamman ma dai mata daga cikin su a wajen ɗaurin auren da kuma wajen zuwa gaishe da iyaye bayan tashi daga wajen da aka ɗaura auren na Ruƙayya Dawayya da Afakallahu.


Jaruman fim sun yi musu fatan alkhairi
Nasiru Salisu Zango na Freedom radio ya samu halartar wannan gagarumin biki inda kuma ya zanta da mutane da dama daga ciki da wajen masana’antar ta Kannywood.
Saratu Gidado, wacce aka fi sani da Daso na daga cikin waɗanda suka samu halartar wannan biki. Tayi ma ango da addu’ar fatan alkhairi da fatan Allah ya basu zaman lafiya a rayuwar auren nasu.
Asma’u Sani ma na daga cikin jaruman fim ɗin da suka halarci wannan taro. An hango ta cikin jaruman da suka halarci gurin bikin don taya ango da amarya murna.


Rashida mai sa’a, wacce mai bada shawara ce ta musamman ga gwamnan jihar Kano, kuma jarumar fim ɗin Kannywood ta samu halartar wannan gagarumin biki.
Rashida ta nuna farin cikin ta kan wannan aure na Ruƙayya Dawayya da Afakallahu, inda ta yi musu fatan alkhairi gami da roƙon Allah yasa auren nasu ya zamto mutu ka raba ne.
Furodusa Abubakar Bashir Mai shadda dai shima ya samu halartar wannan taro inda yace ya cike da matuƙar farin ciki. Yayi addu’ar fatan alkhairi da fatan Allah ya bawa angon da amarya zaman lafiya a cikin auren nasu.
Rabiu Biyora ma ya samu halarta, inda shima ya taya ango Afakallahu da amarya Ruƙayya Dawayya farin cikin wannan rana, gami da yi musu fatan alkhairi. Haka nan ya gode ma waɗanda suka samu halartar wannan ɗaurin aure.
Ado Ahmad gidan Dabino wanda ake kira da gwamnan alfawa shima dai ya samu damar halartar taron inda shima yayi fatan alkhairi ga ango da amarya.


Ruƙayya Dawayya ta yi addu’a ga ‘yan baya
A nata bangaren, amarya Ruƙayya Dawayya ta nuna farin cikinta sosai kan wannan rana, inda ta bayyana cewa gurin ta ya cika data auri Afakallahu, kuma tana roƙon jama’a su taya su da addu’ar Allah ya basu zaman lafiya.
Ta ƙara da yi ma mahalarta taron nasu godiya tare da yi ma sauran waɗanda basu yi auren ba addu’ar samun mazaje na gari musamman ma dai irin nata, kamar yadda tace a hirar ta da freedom radio.
A wani labarin na daban kuma, kunji yadda wani Miji ya kashe matar shi saboda ta bincika mishi waya.
Wani miji ɗan kimanin shekara 37 ya kashe matar shi ta hanyar sarar ta da wuƙa a sassa daban-daban na jikin ta sakamakon binciken da ta yi mishi a cikin wayar shi ba tare da izinin shi ba.
Matar mai suna Mirriam Joni, yar shekara 27 dai bata wuce wata 3 da auran mijin nata ba. Majiyar mu tace ta ɗauki wayar shi sannan ta cire makullin dake kan fuskar wayar, inda daga bisani tayi mishi bincike, wanda a sanadiyyar hakan ne shi kuma ya kashe ta.
Jami’an ‘yan sanda sun tabbatar da faruwar mummunan lamarin wanda ya faru a ƙauyen Matsapa dake yankin Mutasa dake ƙasar Zimbabwe, inda suka bayyana cewa matar ta mutu a nan take.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com