Dakarun sojojin Najeriya sun halaka ƴan bindiga 152 sannan sun lalata sama da sansanin su guda 100 a jihar Kaduna.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, shine ya bayyana hakan inda yace sojojin sun samu wannan nasarar ne a tsakiya da ƙarshen shekarar 2022.
Ya dai bayyana hakan ne a yayin da yake bayar da rahoton yanayin tsaro na tsakiya da ƙarshen shekarar 2022 ga gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai a ranar Juma’ah. Jaridar Vanguard ta rahoto.
An samu gagarumar nasara
“Za ka ga cewa an samu cigaba sosai tun lokacin da sojoji suka ƙara ƙaimi wurin murƙushe ƴan ta’adda a jihar a cikin watanni shida da aka haɗa rahoton.”
“Ƴan ta’adda 152 da ƴan bindiga sojoji suka halaka a jihar, da dama an murƙushe su ne a sansanunuwan su da wajen haɗuwar su.”
“An halaka ƴan bindiga 16 a yankunan ƙananan hukumomin Birnin Gwari da Chikun, yayin da sama da sansanunuwa 100 da ƴan bindiga suke ciki aka lalata su.”
“Sojojin kuma sun ceto mutum 74 da aka yi garkuwa da su.”
Ayyukan ta’addanci sun ragu sosai a jihar
“Kashe-kashe masu alaƙa da ta’addanci da faɗace-faɗace a jihar Kaduna sun ragu matuƙa a ƙarshen shekarar nan. Haka ma an samu raguwar satar mutane da shanaye.”
“Haɗin guiwar da ake yi na haifar da ɗa mai ido. Muna godiya matuƙa ga kwamandoji, da jami’an tsaron da suke aiki ba dare ba rana domin ganin abubuwa sun daidaita. Za mu cigaba da iyaƙar bakin ƙoƙarin mu domin har yanzu akwai sauran aiki.” Inji shi
Sojoji sun halaka ‘yan ta’addan Boko Haram da dama a jihar Borno
Dakarun sojojin Najeriya sun halaka ‘yan ta’addan Boko Haram da dama a wani bata kashi da suka yi a yankin Banki na karamar hukumar Bama ta jihar Borno.
Jaridar The Cable ta rahoto cewa sojojin wadanda suka fito daga bataliya ta 151 tare da hadin guiwar ‘yan sakai (CJTF) sun afkawa maboyar ‘yan ta’addan a kauyen Gauri a ranar 30 ga watan Oktoba
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com