An maka bankin Absa da ke Kenya gaban kotu bayan wani dan kasuwa ya zarge su da bayyana wa wani rashin kudinsa ba tare da saninsa ba, LIB ta ruwaito.
Kirui Kamwibua, mai kamfanin New Mega Africa Ltd yana neman Ksh miliyan 192 a matsayin diyyar asarar da kuma Ksh biliyan 1.2 na rasa kimar da yayi tare da Ksh miliyan 92 ta asarar kadarar da yayi bayan maka wani banki gaban kotu.
Ya bayyana cewa sun nuna wa ma’aikatansa halin talaucin da ya shiga wanda hakan ya janyo illa ga kasuwancinsa.
A cewar Kamwibua, bayan an gabatar musu da bayani dangane da matsin da ya shiga, an kawo cikas ga kasuwancinsa.
Ya ce hakan nuna cewa ma’aikacin bankin da ya bayyana sirrin asusunsa alama ce ta gazawar bankin daga adana sirrin masu ajiya a wurinsu. Kuma hakan keta hakkinsa na sirri ne.
Ya kara da cewa duk da yadda ya dinga neman bankin ta ba shi bashi inda ya dinga kai koma ya ci tura, hakan yasa ya dinga tafka asarar kudin mota.
Yadda aka kore ni daga bankin da naje neman aiki bayan gano na taba zaginsu a Twitter, Matashi
Wani matashi ya koka bayan bankin Zenith sun ki amincewa su tattauna da shi saboda wata wallafar da yayi shekaru 2 da su ka gabata yana sukar bankin, Legit.ng ta ruwaito.
A cewar mutumin, yayin da yaje a tattauna da shi wurin aikin, wata mata daga bangaren HR ta nuna masa wata wallafa da yayi shekaru biyu da su ka gabata.
Wannan dalilin yasa ya bukaci mutane da su yi taka-tsantsan akan abubuwan da su ke wallafawa a shafukansu. Matashin mai amfani da suna @djbantiben1 ta bayyana artabun da su ka yi bayan Zenith Bank sun ki ba shi gurbin aiki saboda wani wallafa da yayi a Twitter shekaru biyu da su ka gabata.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com