Rundunar ‘yan sandan Jihar Akwa Ibom ta yi ram da wani Sunday Etukudo bisa zarginsa da halaka diyarsa mai shekaru 20, Ifonmbuk Sunday, akan wata hayaniyar da su ka samu ta cikin gida, Daily Nigerian ta ruwaito.
Kakakin rundunar, SP Odiko Macdon, a wata takarda wacce ya gabatar wa manema labarai a Uyo, ya bayyana yadda ake zargin mamaciyar ta damukar al’aurarsa bayan ya yi amfani da sanda ya buga mata a kai.
Bayan aikata laifin, Mr Etukudo ya birne yarinyar a gidansu da ke kauyen Omum Unyiam da ke karamar hukumar Etim Ekpo don rufe laifinsa d Daga bisani ‘yan sanda su ka tono gawarta don su gudanar da bincike.
A wata takarda wacce ta bayyana yadda a ranar 9 ga watan Oktoba ga aikata laifin ga diyarsa an samu bayani akan yadda kafin nan su ka samu rikici.
Ban ga amfanin barinta ba: Bayan yi masa ɗaurin rai da rai, mutumin ya datse mazakutarsa
Wani mutum ya datse mazakutarsa bayan kotu ta yanke masa hukuncin daurin rai da rai. Mutumin mai suna Henry Hodges ya yanke wannan shawarar cikin bacin rai, LIB Ta ruwaito.
An yanke masa hukuncin ne bayan ya halaka wani mai gyaran waya a shekarar 1992. Ana zargin abinda ya hassala Henry shi ne yadda ya bukaci lauyansa ya kai masa abinci na alfarma a gidan yarin amma jami’ai su ka hana shi ci.
Da farko akan kisan da yayi, an yanke masa shekaru 40 ne, daga bisani kuma aka gane cewa shi ne ya halaka wani injiniya a wani otal da ke Atlanta.
Lauyansa ya kai masa ziyara Cibiyar Tsaro ta Riverbend Maximum a Nashville, inda ya je masa da abincin, sai dai an hana shi amsa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com