27.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Saboda talauci yayi min katutu tsohon saurayina ya rabu dani, yanzu ɗaya daga cikin ma’aikata na yake aure

LabaraiSaboda talauci yayi min katutu tsohon saurayina ya rabu dani, yanzu ɗaya daga cikin ma'aikata na yake aure

Wata mata ƴar Najeriya mai suna Aisha Umar Jajere, ta bayyana yadda tsohon saurayin ta ya watsa ta a kwandon shara shekara biyar da suka wuce saboda talauci yayi mata katutu.

Aisha ta bayyana hakan ne a wani rubutu da tayi a shafin ta na Twitter.

Tsohon saurayin nata yanzu ma’aikaciyar ta yake aure

A cewar ta tsohon saurayin na ta da ya guje ta yanzu haka ɗaya daga cikin ma’aikatan ta yake aure.

Ta dai tuno wannan halin da ta shiga ne a baya yayin da ta sanya wani tsohon hotonta sanye da kayan masu yiwa ƙasa hidima (NYSC) da kuma wani sabon hotonta na yanzu.

Aisha tayi wannan rubutun ne a ranar Laraba 2 ga watan Nuwamban 2022.

A kalamanta:

“Ina da wani labari da zan gaya muku dangane da ni amma a taƙaice. Yadda abin yake shine,,,, shekara biyar da suka gabata ya watsar da ni saboda talauci ya min katutu,,, yanzu yana auren ɗaya daga cikin ma’aikata na. Rayuwar nan akwai abin mamaki.”

Mutane sun tofa albarkacin bakin su

@DoubleDeez_umar ta rubuta:

“Hahha kenan dai a jininsa ba na arziki.
Bai de samun me kuɗin ba”

@DanBarrister001 ta rubuta:

“Hakan na nufin dai haryanzu kina jin zafin abin kenan, gashi duk kudin ki ya miki tsada, amma maza basa rabuwa da mace don kawai talaka ce, dole akwai wani abu dai. Shawara kije kawai ki rokeshi ya yarda ki zama ta Biyu….”

Mutane suna yaba kyawuna, amma duk da haka na kasa samun saurayi – matashiya

A wani labarin na daban kuma, wata matashiya ta koka saboda ta kasa samun saurayi.

Wata matashiya mai tashe a soshiyal midiya ta koka kan yadda ta gaza samun tsayayyen saurayi duk da tarin mabiya da take da su a shafukanta na sada zumunta na zamani. 

Matashiyar mai amfani da suna Ms PuiYi a shafukan sada zumunta ‘yar shekara 24 ta koka kan yadda mutane da dama ke yabawa da irin kyawun da take dashi, amma kuma bata da tsayayyen saurayin da zata yi tarayya dashi a rayuwarta, majiyar mu ta wallafa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe