24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

An dakatar da wani likitan Birtaniya mai cewa musulmai mata su cire hijaban su

LabaraiAn dakatar da wani likitan Birtaniya mai cewa musulmai mata su cire hijaban su

An dakatar da wani likita ɗan ƙasar Birtaniya na wata tara daga aiki bayan ya buƙaci wata mara lafiya musulma ta cire hijabin ta har sau uku a lokacin da yake dubata.

Masu bincike sun yanke shawarar dakatar da Dr. Keith Wolverson, wanda ya kwashe shekara 25 yana aikin likitanci, na wani ɗan lokaci inda suka kira abinda ya aikata a matsayin abin baƙin ciki. Jaridar The Islamic Information ta rahoto.

An bayyana laifukan da ake tuhumar sa da su

Wasu daga cikin laifukan da likitan ya aikata sun haɗa gayawa matan aure musulmai su cire hijaban su. Ya kuma caccaki yadda wasu mara lafiya sha biyar ke yin turanci.

Duk da cewa ya yarda abinda ya aikata ya saɓawa ƙwarewar aiki, Dr. Wolverson yace yana da shirin ɗaukaka ƙara kan hukuncin da aka yanke masa na hana shi aiki a matsayin likita har na tsawon wata tara.

Kotun tace likitan ya aikata abin baƙin ciki

A lokacin zaman kotun ma’aikatan lafiya, an samu Dr. Wolverson ya amsa laifuka 17 cikin laifuka 28 da ake tuhumar sa da su.

Zarge-zargen saɓawa ƙa’idar aiki da aka yiwa likitan sun faro ne tun daga watan Mayun 2018 a wasu wurare uku da yake aiki.

Mai shari’a Duncan Toole yace shaidu sun nuna cewa abin da Wolverson ya aikata abin baƙin ciki ne sannan hakan zai iya sanya wa mutane rasa ƙwarin guiwa a kan aikin likitanci.

Sai dai kotun tayi nuni da cewa likitan bai da wata matsala dangane da kare lafiyar marasa lafiya a shekara 25 da yayi yana aiki.

An yi ram da likitan da ya yiwa mai ciki fyade tana tsaka da nakuda

An kama wani likita da ake zarginsa da yiwa wata mata mai juna biyu fyade yayin yi mata aiki, sannan anyi imani da wata kila ya yiwa wasu mata biyun a wannan ranar, LIB ta ruwaito

Anyi ram da Giovanni Quintella Bezerra mai shekaru 32 bisa zarginsa da laifin fyade bayan an dauki bidiyonsa a boye yana yiwa wata mata fyade ta baki bayan ya mata allurar bacci a asibitin Mulher na São João de Meriti, Rio de Janeiro.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe