35.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Qatar ta kawata hanyoyin zuwa filin kwallon FIFA da hadisan Manzon Allah (S.A.W)

LabaraiLabaran DuniyaQatar ta kawata hanyoyin zuwa filin kwallon FIFA da hadisan Manzon Allah (S.A.W)

Ƙasar Qatar ta ƙawata hanyoyin zuwa filin da za’a gudanar da wasan cin kofin duniya na FIFA da hadisan Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama.

FIFA ta zaɓi Qatar a wannan zagayen

Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya wato FIFA dai ta zaɓi ƙasar ta Qatar a matsayin wacce zata ɗauki nauyin gasar cin kofin duniya na ƙwallon ƙafan da zai gudana na bana.

A ƙoƙarin ƙasar na nuna al’adunta da addinin ta, Qatar ta ƙawata hanyoyin cikin biranen da za’a gudanar da wasan, wato a biranen Doha, Lusail da Al khor da kayayyakin ƙyale-ƙyale iri daban-daban. Daga ciki akwai allunan dake ɗauke da hadisan Manzon Allah (S.A.W), a gurare da dama.

An rubuta hadisan Manzon Allah akan bangwaye

Wasu na ganin cewa hakan da Qatar ɗin tayi wata hikima ce ta tallar addinin musulunci da kuma kyawawan dabi’un Annabi (S.A.W) ga magoya bayan ‘yan ƙwallon da zasu zo kallon gasar, wacce take gudana a duk bayan shekara huɗu.

fifa 2022 world cup prophet muhammad hadiths qatar3 1024x768 1

Allunan jikin bangon da aka yi rubutun sun ƙunshi Hadisan Manzon Allah (S.A.W) waɗanda aka fassara su da harshen turanci. Mafi yawan hadisan dai suna magana ne akan tausayi, sadaƙa da kuma ƙarfafa ma mutane gwuiwa akan suyi ayyuka na ƙwarai.

fifa 2022 world cup prophet muhammad hadiths qatar2 1024x768 1

Daga cikin hadisan akwai wanda ke magana akan “dukkan wani kyakkyawan aiki sadaqa ne” , haka nan akwai hadisin nan dake nuna muhimmancin girmama maƙwabci da kuma karrama baƙo.

Ana sa ran fara buga wannan gasa ta kofin duniya a ranar 20 ga watan Nuwamba da muke ciki, wanda za’a yi har zuwa 18 ga watan Disamban wannan shekara.

fifa 2022 world cup prophet muhammad hadiths qatar1 1024x768 1

Qatar na fuskantar suka daga ƙasashen duniya

Wannan ne dai karo na farko da aka taɓa kawo wasan zuwa gabas ta tsakiya, kuma ƙasar musulmai, sannan kuma a watanni biyu na ƙarshe shekara.

Qatar ta kashe maƙudan kuɗaɗe wajen ganin an kawo gasar zuwa ƙasar ta. Sai dai suna shan suka daga ƙasashen duniya bisa ƙorafin cewa suna yawan take haƙƙin ɗan adam, zarge-zargen da Qatar ɗin tace da wasu manufofi kawai ake yin su.

A wani labarin na daban kuma, kunji cewa a yau juma’a ne dai jaruma Rukayya Dawayya zata angwance da angon ta Afakallahu.

Fitacciyar jarumar masana’antar fina-finann Hausa ta Kannywood Ruƙayya Umar Santa wacce aka fi sani da ruƙayya Dawayya zata angwance da Shugaban hukumar tace finafinai ta jihar Kano, Isma’ila Na’abba Afakallahu.

Wani katin gayyata data wallafa a shafin ta na Instagram kwana uku da suka wuce ya nuna cewa yau juma’a, 04 ga watan Nuwamban nan da muke ciki, da misalin ƙarfe biyu na rana ne za’a ɗaura auren jaruma Ruƙayya Dawayya da angon nata a masallacin  dake nan cikin birnin Kano.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe