Fitacciyar jarumar masana’antar fina-finann Hausa ta Kannywood Ruƙayya Umar Santa wacce aka fi sani da ruƙayya Dawayya zata angwance da Shugaban hukumar tace finafinai ta jihar Kano, Isma’ila Na’abba Afakallahu.
Ta wallafa katin gayyata a shafin ta
Wani katin gayyata data wallafa a shafin ta na Instagram kwana uku da suka wuce ya nuna cewa yau juma’a, 04 ga watan Nuwamban nan da muke ciki, da misalin ƙarfe biyu na rana ne za’a ɗaura auren jaruma Ruƙayya Dawayya da angon nata a masallacin dake nan cikin birnin Kano.
Baya ga wannan kuma, jarumar ta ƙara wallafa wani ɗan takaitaccen bidiyo na gayyatar ɗaurin auren wanda kuma aka wallafa shi a gidan talabijin na NTA a shafinta na Instagram daga baya bayan nan.
Ruƙayya Dawayya da Afakallahu sun daɗe suna soyayya
Batun soyayya tsakanin jaruma Ruƙayya Dawayya da shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano Isma’il Afakallahu ba wai wani sabon batu bane, musamman ma dai ga masu bin jarumar a shafukan ta na sada zumunta zasu riƙa ganin yadda yake yawan wallafa hotunan sa na yabo da makamantansu.

Dawayya ta na yawan wallafa hotunan Afakallahu, hotunan ‘ya ‘yanshi da kusan duk wasu abubuwa da suka shafe shi irin su batutuwan siyasa da sauran abubuwa na yau da kullum a shafukan ta na sada zumunta.
Duk da dai ance soyayya tsakanin Ruƙayya Dawayya da Afakallahu ba yanzu aka fara ba. Sun daɗe suna soyayyar su a sirrance ba tare da bayyana ma jama’a ba. Daga bayan nan ne da abun ya matso jarumar ta riƙa bayyana ma jama’a ta hanyar sanya wa a kafafen sadarwar zamani.
Ta buƙaci jama’a suyi musu addu’a
A ƙasan katin gayyatar da ta ɗora a shafin nata na Instagram, Ruƙayya Dawayya ta roƙi waɗanda ba zasu sami damar zuwa ba da su yi musu addu’a ta fatan alkhairi.
“Alhamdulilah muna gayyatar ‘yan uwa da abokan arziki. Idan ba’a samu dama ba, ayi mana addu’a.” Jarumar ta rubuta.
A wani labarin na daban kuma, wata matashiya mai tashe a soshiya midiya ta koka kan yadda ta gaza samun tsayayyen saurayi duk da tarin mabiya da take da su a shafukanta na sada zumunta na zamani.
Matashiyar mai amfani da suna Ms PuiYi a shafukan sada zumunta ‘yar shekara 24 ta koka kan yadda mutane da dama ke yabawa da irin kyawun da take dashi, amma kuma bata da tsayayyen saurayin da zata yi tarayya dashi a rayuwarta.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com