Wata matashiya mai tashe a soshiyal midiya ta koka kan yadda ta gaza samun tsayayyen saurayi duk da tarin mabiya da take da su a shafukanta na sada zumunta na zamani.
Matashiyar mai amfani da suna Ms PuiYi a shafukan sada zumunta ‘yar shekara 24 ta koka kan yadda mutane da dama ke yabawa da irin kyawun da take dashi, amma kuma bata da tsayayyen saurayin da zata yi tarayya dashi a rayuwarta, majiyar mu ta wallafa.
Ms PuiYi, wacce ‘yar asalin birnin Kuala Lumpur ne wato babban birnin ƙasar Malesiya ta samu tarin mabiya a shafukan ta na Tiktok, Facebook da kuma Instagram, inda take yawan wallafa hotunan ta ga mabiyan nata.
Tana daga cikin masu tashe a yankin Asiya
Ms PuiYi tana daga cikin mutanen da aka fi binciko sunan su a kafafen sada zumunta na yankin Asiya. Tana da aƙalla mabiya miliyan ashirin a shafinta na Instagram, tana da kuɗi kuma tayi suna, amma duk da haka ta gagara samun masoyi na gaskiya.
Matashiyar ta ƙara da cewa takan tsinci kanta a halin kaɗaici sakamakon gaza samun masoyi na gaskiya wanda ya dace da ita ba wai kawai wanda zai zo ya biya buƙatun shi da ita ba ya ƙara gaba ba.
Abu ne mai wahala ka samu masoyi na gaskiya
“Abu ne mai matuƙar wahala da matuƙar aiki kan samun ainihin mutumin daya dace. Ina son samun soyayya ta gaskiya bawai soyayyar jin daɗin juna ba.” inji matashiyar.
Ta kuma ƙara da cewar yanzu tana da abubuwa da dama a gabanta, a sabili da haka ba za ta iya cigaba da jurar raɗaɗin rabuwa da kuma kasa samun isasshen barci ba a dalilin samarin da basu dace da ita ba.
“Ina da burika da dama da nake son cimma wa a yanzu. Bazan iya cigaba da jure ciwon rabuwa da kuma gaza sukuni da samun barci saboda wani can da ma bai dace da ni ba.” inji ta.
Matashiyar ta baiwa ‘yan mata shawara
Ms PuiYi ta ƙara da cewar ta ɗan yi soyayya da samari da dama amma har yanzu dai bata samu wanda ya kwanta mata a rai ba.
Ta baiwa ‘yan mata shawara akan su daina yarda da samarin dake zuwa suna fasa musu kai da cewa su kyawawa ne suna cika su da yabo da daɗin baki don kawai su faɗa soyayya da su.
A wani labarin kuma, kunji yadda wata mata ta bayyana yadda take shan tsangwama daga mutane kan saje da gemu da ke yawan fito mata.
Wata mata ta bayyana yadda take fuskantar tsangwama da tono daga wajen mutane sakamakon yadda saje da kuma gemu ke fito mata a fuska kamar yadda yake fito ma maza.
Matar mai suna LaRae Perkins, yar California dake ƙasar Amurka dai na fama da wata matsala ce daga jikin sinadaran da ke taimaka wa fitar da gashi na jikin ɗan adam waɗanda ke sanya ta fitar da gashi na saje da gemu kamar yadda maza ke fitarwa.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com