Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ƴan Najeriya ba su da wani dalilin da zai sanya su yi ƙorafi akan yunwa bayan ƙasar nan Allah ya albarkace ta ƙasar noma.
Jaridar Daily Nigerian ta rahoto shugaba Buhari ya bayyana hakan a wata hira da gidan talabijin na Tambari Hausa TV yayi dashi wacce haka watsa a daren ranar Laraba.
Da yake amsa tambaya kan yawaitar yunwar da ake fama da ita a ƙasar nan, shugaba Buhari sai ya kada baki yace duk wanda yake jin yunwa da gaske zai ɗauki kayan aikin sa ne ya nufi gona.
Shugaba Buhari yace tsare-tsaren da gwamnatin sa ta kawo sun haifar da ɗa mai ido
A cewar sa, kulle iyakokin ƙasar nan da wasu shirye-shiryen da gwamnatin sa ta ƙirƙiro domin ganin an samu wadatuwar abinci sun haifar da ɗa mai ido.
“Idan kana ƙoƙarin ka gaya wa ƴan Najeriya cewa na kasa cika alƙawarin da na ɗauka, bari na tambayeka, lokacin da na hau mulki ban bayar da umurnin a kulle iyakokin ƙasar nan har na tsawon shekara biyu ba?,” Inji shugaba Buhari.
“Na ɗauki wannan matakin na hana shigo da shinkafa sannan nace mu noma abinda zamu ci ko mu mutu da yunwa.”
“Na ce tunda muna da ƙasar noma kuma Allah ya albarkace mu da ruwan sama, wane dalili ɗan Najeriya yake da shi na cewa yana jin yunwa? Idan kana jin yunwa, ka tafi gona.”
An samu nasara sosai a cewar sa
Shugaba Buhari ya kuma cigaba da cewa:
“Ina sane da cewa ambaliyar ruwa ta lalata wasu gonakin a wannan daminar, amma kuma har yanzu muna siyar da shinkafa ƴar Najeriya, sannan za mu iya ciyar da kan mu. Shin wannan ba nasara ba ce?”
“Muna da ma’aikata waɗanda suka bar ƙayatattun ofisoshin su, suka koma gona, kuma sun samu amfani mai yawa. Don haka mun gode sosai.”
Na gaza a matsayin ministan Buhari -Adamu Adamu
Mallam Adamu Adamu, ministan ilmi na tarayyar Najeriya, ya yanke wa kansa hukunci kan naɗin da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yayi masa a shekarar 2015.
Adamu Adamu a ranar Alhamis uku ga watan Oktoba 2023, ya aminta cewa a matsayin sa na ministan da yafi kowa daɗewa a gwamnatin Buhari, ya gaza wajen shawo kan matsalolin da suka addabi ministirin ilmi.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com