Wata mata ta bayyana yadda take fuskantar tsangwama da tono daga wajen mutane sakamakon yadda saje da kuma gemu ke fito mata a fuska kamar yadda yake fito ma maza.
Matsalar daga jikin sinadaran jikinta suke
Matar mai suna LaRae Perkins, yar California dake ƙasar Amurka dai na fama da wata matsala ce daga jikin sinadaran da ke taimaka wa fitar da gashi na jikin ɗan adam waɗanda ke sanya ta fitar da gashi na saje da gemu kamar yadda maza ke fitarwa.
Tace tun tana ‘yar shekara goma sha biyu ne dai likitoci suka tabbatar mata da tana da wannan matsala, inda suka bayyana mata cewa tana ɗauke da sinadarai na maza da yawa, kamar yadda majiyar mu ta wallafa.
Gemun ya janyo mata tsangwama da kaɗaici
LaRae tace hakan ya janyo mata tsangwama ta hanyar yadda mutane ke yawan yi mata tambayoyi na izgilanci akan cewa ita mace ce ko kuma namiji sakamakon saje da gemun dake yawan fito mata tun a lokacin.

Matar ta ƙara da cewar a wancan lokacin ta sha zama cikin takura, cikin kaɗaici, jin kunya da kuma jin ta fita daban cikin jama’a tunda aka tabbatar mata da wannan matsala a cikin halittar ta.
Ta kuma bayyana cewa a lokacin da ta fara jinin al’ada ya rinƙa zo mata da matsala wacce har sai da likitoci suka ɗora ta akan maganin taƙaita haihuwa.
Da farko ta fara ƙoƙarin rinƙa aske sajen ko gemun dake fito mata, amma sai ta fuskanci hakan na yawan janyo mata matsala a fatar fuskarta. Daga baya sai kawai ta yanke shawarar barin gashin ya fito yadda yake so.

Yanzu bata jin kunyar barin gemun
A yanzu bata jin kunyar barin gashin dake fitowa a fuskarta, kuma yanzu haka ta na jagorantar matan dake fuskantar makamanciyar irin matsalar tata inda a yanzu haka ma take sanya kayan dake ɗauke da rubutun cewa ‘ni mace ce’.
Sannan kuma ta ƙara da cewar yanzu bata wani ƙoƙarin asken gashin dake fito mata ko kuma ƙoƙarin sanya mishi wani magani don kar ya fito. Tace hakan na janyo mata matsaloli a fuskar tata.
A wani labarin na daban kuma, kunji labarin yadda harbin kunama yayi sanadiyyar mutuwar mutane 2 a Sokoto.
A daren ranar Lahadin da ta gabata ne dai muka samu labarin wata kunama da ta yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu daga cikin mutane biyar da ta harba a yayin da suke tsaka da hira, a yankin Arkiila dake Sokoto.
Wannan mummunan lamari dai ya faru ne a lokacin da mutanen ke tattauna batutuwan da suka shafi ƙasa a irin hirar majalissar da ake yi da dare, kamar yadda majiyar mu ta wallafa.
Wani mutum mai suna Alhaji Abubakar wanda lamarin ya faru a gaban shi ya bayyana cewa da farko da suka ga abun ya taho basu ɗauka cewa kunama bace. Sun yi zaton cewa kyankyaso ne ke yawo, a sabili da haka basu wani maida hankali akai ba.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com