Jaruma Amal Umar ta Kannyood ta bukaci kotu ta dakatar da mataimakin sifetan ‘yan sanda wanda yake kulawa da yanki na daya da kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Kano da kuma wani dan sanda mai bincike kama ta, Freedom Radio ta ruwaito.
Amal ta bukaci hakan ne ta hanyar shigar da korafi a kotun jiha mai lamba 17 da ke titin Miller a Kano.
Rahotanni sun nuna yadda ‘yan sandan su ka bazama nemanta bisa zargin damfarar da ake wa saurayinta Ramadan.
Wani Alhaji Yusuf Adamu ya kai korafi ga ‘yan sanda inda ya bayyana musu zargin da yake yi wa Ramadan na damfararsa miliyan 40 wadanda yace zai sanya a kasuwancin waya.
Bayan kama Ramadan ne ya bayyana cewa ya siya wa jaruma Amal din mota tare da zuba mata kayan Naira miliyan biyar a shagon da ya bude mata.
A cewarsa ya bata Naira miliyan uku daban don ta ba mahaifinta ya biya wasu basuka da ake binsa.
Ya ce akwai wasu kudade na daban da yayi mata transfer dinsu. Wannan yasa ‘yan sandan su ka kama jarumar tare da amshe mata motar tare da ci gaba da bincike akanta.
Hakan ya da tayi gaggawar bazama kotu. A zaman ranar Alhamis da aka yi a kotu, lauyan Alhaji Yusuf, Barista Yusuf Dan Sulaiman ya bukaci a sanya su cikin masu kara.
Mai shari’a Sunusi Ado Ma’aiki ya dage sauraron karar zuwa ranar 16 ga watan Disamba don duba bukatarsu.
Na sanya gidaje na kasuwa, na siyar da mota ta don fanso yara na gurin masu garkuwa
Mutumin mai suna Lukman Aliyu, mai sana’ar kayan ƙarafa, wanda mazaunin garin Ilorin jihar Kwara ne, ya bayyana ma jaridar Punch cewa sai da ya sanya gidajen shi guda biyu a kasuwa, haka nan ya siyar da motar shi da kuma wasu kayayyaki kafin ya iya haɗa kuɗin da zai fanso ‘ya ‘yan shi.
Masu garkuwa da mutane sun ɗauke ‘ya ‘yan na shi Muhiddeen ɗan shekara 15 da kuma Abdulƙadir dan shekara 12 a ranar 13 ga watan Oktoban nan da muke ciki a gidansu dake Aseyori, yankin Alagbado dake ƙaramar hukumar Ilorin ta kudu dake jihar Kwara.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com