36.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Wani lokacin ƴan iskan maza sun fi iya soyayya, Fatima Umar

LabaraiWani lokacin ƴan iskan maza sun fi iya soyayya, Fatima Umar

Wata budurwa ma’abociya amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Twitter mai suna Fatima Umar ta bayyana irin mazan da su ka fi iya soyayya.

Yayin da mata da dama ke neman maza natsatstsu da hankali, ita ra’ayinta dangane da maza wadanda su ka fi lakantar soyayya.

Budurwar wacce tayi wallafar tare da hadawa da wani hotonta wanda ta dau kyau, ta bayyana cewa maza ‘yan iska sun fi iya soyayya.

A cewar Fatima, wani lokacin maza ‘yan iska sun fi iya soyayya maimakon maza masu natsuwa.

Kamar yadda ta wallafa:

Wani lokacin ‘yan iskan maza sun fi iya soyayya.

Tabbas wannan wallafar ta dauki hankali kwarai, inda wasu ke ganin gaskiya maganarta, wasu kuma na ganin akasin haka.

Wawaye ne ke auren soyayya, saboda kudi zan yi aure, Cewar amarya Habiba

Wata amarya mai suna Habiba Gado ta wallafa hotunanta a Facebook na kafin aurensu ne tare da angonta wanda taken da ta yi wa hotunan ya yi matukar daukar hankulan mutane da dama.

Aure saboda kudi zan yi, babu abinda ya dame ni da shirmenku, a cewarta.

Ta kara da cewa “Wawaye ne ke auren soyayya.”

Ba dai a tabbatar ko wasa take yi ba ko kuma da gaske take kuma har yanzu har yanzu bata bi bayan wallafar tara yi wata wallafar wacce za ta wanke waccan ba duk da fiye da mutane 2,000 sun yi ta tsokaci.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe