Wata budurwa mai suna Oghadeva Sandra ta koka kan yadda saurayin ta da suka kwashe shekara biyu suna kwasar ƙauna ya rabu da ita ya auri wata daban.
Sandra ta bayyana yadda tayi ta haƙuri ta zauna tare da shi har na shekara biyu duk kuwa da cewa lokacin da bai da ko sisi.
Budurwar ta koka kan yadda ya auri wata daban ba ita ba
Abin takaicin yana fara samun kuɗaɗe, sai ya watsar da ita ya auri wata daban. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
Da take bayar da labarin halin baƙin cikin da ta shiga, budurwar ta rubuta a shafinta na Twitter cewa:
“Nayi soyayya da saurayin da baya da ko sisi har na shekara biyu, har amanata yake ci amma ban damu ba, yana fara samun kuɗi ya auri wata daban, don haka wacce irin shawara za ku bani?
“Yanzu haka yana da aure amma yana tuntuɓata wasu lokutan, har so yayi mu haɗu a wani lokaci amma naƙi yarda, idan har hali na baya da kyau meyasa har yanzu zar riƙa tuntuɓata?”
Mutane sun bayyana ra’ayoyi mabambanta
Archangel Gabriel ya rubuta:
“Zan iya rantsuwa cewa ke ma a shekara biyun da kuka yi tare kin ci amanar sa sosai sannnan kinyi tunanin bai sani ba. Wannan shine abinda ya sanya ba ke ya aura ba.”
Muhphasa ya rubuta:
“Ki manta kawai Sandra, ta iya yiwuwa ba ki da rabon shan wahala ne baki sani ba. Ina rokon ubangiji ya baki wanda ya fi shi.”
Top Notch ya rubuta:
“Namiji ya san inda zuciyar sa take, ta iya yiwuwa kawai yayi amfani dake ne kawai amma baki da halayen da yake so a jikin matar da zai aura.”
Warin ruɓaɓɓen kwai take yi, Cewar matashi bayan budurwarsa ta dawo kwana ɗakinsa
Wani matashi ya bayyana halin da yake ciki yanzu haka bayan budurwarsa wacce su ka yi shekaru uku tare ta dawo dakinsa inda ya koma kwana akan kujera, Legit.ng ta ruwaito.
Matashin ya ce bai gano cewa budurwarsa warin rubabben kwai take yi ba sai da ya dawo da ita dakinsa inda ya gane cewa tana daukar kwanaki kafin tayi wanka
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com