Mallam Adamu Adamu, ministan ilmi na tarayyar Najeriya, ya yanke wa kansa hukunci kan naɗin da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yayi masa a shekarar 2015.
Adamu Adamu duk da yafi kowane minsta daɗewa amma sai gashi ya gaza
Adamu Adamu a ranar Alhamis uku ga watan Oktoba 2023, ya aminta cewa a matsayin sa na ministan da yafi kowa daɗewa a gwamnatin Buhari, ya gaza wajen shawo kan matsalolin da suka addabi ministirin ilmi.
Ministan yayi nuni na musamman kan cewa tun daga kan yawan yaran da basa zuwa makaranta wanda yawan su ya ƙaru sosai a lokacin sa, da yajin aikin ƙungiyar malaman jami’a (ASUU) da sauran matsalolin da suka mamaye ɓangaren ilmin gaba da sakandire, ya kasa samar da maganin matsalolin. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
Ministan ya bayyana waɗanda suka taimaka ya samu koma baya
Adamu yayi wannan tonon sililin ne a wurin taron a ‘National Council on Education’ (NCE) karo na 66 a birnin tarayya Abuja, inda ya kuma zargi ministirin ilmi na jihohi da taimakawa wajen gazawar sa a matsayin minista.
Najeriya za ta zama babbar mai samar da iskar gas zuwa kasashen Ketare– cewar ministan man Fetur Sylva
A wani labarin na daban kuma, ƙaramin ministan man fetur yace nan bada daɗewa ba Najeriya zata fara samar da iskar gas.
Karamin ministan albarkatun man fetur Timipre Sylva, ya ce Najeriya na shirin zama babbar mai samar da iskar gas a Turai, sakamakon matsalar makamashin da ake fama da shi a duniya, sakamakon rikicin da ake ci gaba da yi tsakanin Rasha da Ukraine.
Mista Sylva ya bayyana haka a ranar Talata yayin wani taron koli a bikin cika shekaru 50 na Gastech Conference 2022 a Milan, Italiya.
Mai taken: “Energy Transition for Developing Nations.”
Ministan ya ci gaba da cewa, a halin yanzu, tallafin da ake samu na bunkasa iskar gas ya kasance nasara ga Turai da Afirka
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com