A daren ranar Lahadin nan da ta gabata ne dai muka samu labarin wata kunama da ta yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu daga cikin mutane biyar da ta harba a yayin da suke tsaka da hira, a yankin Arkiila dake Sokoto.
Mutanen suna kan tattauna lamurran ƙasa
Wannan mummunan lamari dai ya faru ne a lokacin da mutanen ke tattauna batutuwan da suka shafi ƙasa a irin hirar majalissar da ake yi da dare, kamar yadda majiyar mu ta wallafa.
Wani mutum mai suna Alhaji Abubakar wanda lamarin ya faru a gaban shi ya bayyana cewa da farko da suka ga abun ya taho basu ɗauka cewa kunama bace. Sun yi zaton cewa kyankyaso ne ke yawo, a sabili da haka basu wani maida hankali akai ba.
Ya bayyana cewa ba’a jima ba, can sai wani daga cikin mutanen majalissar mai suna Mubarak ya yi ƙorafin cewa ya na da jin zafi a ƙafar shi ta dama, daga nan kuma sai ya fara fitar da wata irin matsananciyar zufa.
Basu iya gano cewa kunama ce ba
Ya ƙara da cewar ba’a jima da wannan ba kuma sai wani ma yace shima fa yaji an cije shi, daga nan ne suka tashi suka fara haske-haske domin su gano ko menene, amma hakan ya ci tura. Ashe duk wannan kunamar ce ta ke ta harbin su.
Bayan haka, Alhaji Abubakar yace sun yanke shawarar canja gurin zaman, wanda ɗan taƙi ne kaɗan daga inda suke, wanda ba da jimawa ba kunamar ta ƙara zuwa ta harbi wani a nan ma.
An garzaya da mutane uku asibiti
Daga nan ne dai kuma sai abun yayi ƙamarin da yayi sanadiyyar mutuwar mutane biyun da ta harba da farko. Sauran mutane ukun kuma sun garzaya zuwa wani kyamis inda aka shawarce su da su wuce asibiti don samun cikakkiyar kulawa.
A wani labarin na daban kuma, kunji yadda wata mata ta kashe kanta saboda mijin ta zai ƙara aure.
Ana zargin cewa wata mata mai suna Yetunde Folorunsho ta kashe kanta ta hanyar shan gubar maganin ƙwari domin ta hana mijin ta mai suna Dare Araoje ƙara aure.
Dailytrust ta wallafa cewa wannan lamari dai ya faru ne a garin Ilorin na jihar kwara inda matar wacce take da ‘ya ‘ya guda biyu tare da mijin ta suke zaune.
Mai magana da yawun hukumar ‘yan sanda na jihar kwara Ajayi Okasanmi ya shaidawa manema labarai cewa binciken da suka gudanar akan gawar matar ya tannatar da cewa lallai ta sha maganin ƙwarin nan ne da ake kira da ‘sniper’ wanda shine yayi ajalin nata.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com