Wata mata ta bayyana yadda gabadaya ta sauya bayan rabuwar aurenta da tsohon mijinta wanda su ka kwashe shekaru 18 takwas. Matar mai shekaru 42 ta wallafa hotunanta wanda yanzu ta fara dawowa da gwabinta, LIB ta ruwaito.
A shekarar 20220 su ka rabu, yanzu kuwa ta koma shar kamar ba ita bace a baya. Cikin shekaru har ta dawo da kumarinta.
Matar mai yara biyu ta koma tana motsa jiki tare da neman abinci mai gina jiki. A cewarta yanzu maza har rububinta idan ta fita.
A cewarta:
“A baya na koma tamkar fanko na tsotse duk na sukurkuce, amma yanzu ina more rayuwa. Ina cikin farinciki kuma na sauya.“
Sun yi aure ne a shekarar 2000, lokacin tana da shekaru 22. A cewarta ta fara shiga tashin hankali ne shekaru da dama da su ka gabata.
A shekarar 2021 su ka karkara rabuwa, a watan Oktoba su ka guntule gabadaya. Ta ce bayan rabuwarsu ta sauya sutturu ta siyo masu kyau.
Ta fara kwalliya sannan ta dena shan kayan shaye-shaye na hayaki. Ta ce ta koma cin kwai da dankalin turawa tare da cin kaji da sauran kayan dadi.
Wata mata ta kashe kanta saboda mijin ta zai ƙara aure
Ana zargin cewa wata mata mai suna Yetunde Folorunsho ta kashe kanta ta hanyar shan gubar maganin ƙwari domin ta hana mijin ta mai suna Dare Araoje ƙara aure.
Lamarin ya faru a Ilorin jihar Kwara
Dailytrust ta wallafa cewa wannan lamari dai ya faru ne a garin Ilorin na jihar kwara inda matar wacce take da ‘ya ‘ya guda biyu tare da mijin ta suke zaune.
Mai magana da yawun hukumar ‘yan sanda na jihar kwara Ajayi Okasanmi ya shaidawa manema labarai cewa binciken da suka gudanar akan gawar matar ya tannatar da cewa lallai ta sha maganin ƙwarin nan ne da ake kira da ‘sniper’ wanda shine yayi ajalin nata.
Matar, wacce tayi digirin ta a bangaren nazarin yaruka, wacce kuma ‘yar asalin jihar Osun ce ta mutu ne a lokacin da ake kan hanyar kaita asibitin gwamanti dake garin Ilorin.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com