Wani ango ya dauko amaryar sa akan babur domin zuwa wajen daurin auren su. Mutane da dama sun tofa albarkacin bakin su akan bidiyon.
A wani bidiyon da wani mai amfani da @Mujunimedardmujuni ya saka a TikTok, angon cikin kasaita ya dare kan babur din tare da amaryar sa da kuma babbar kawar amarya. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
Alamu sun nuna cewa angon da amaryar sa suna kan hanyar su ta zuwa wurin daurin auren su ne.
Amaryar tayi ado cikin kayan amare yayin da ango shima ya sha kwalliya cikin kayan angwanci.
Sai dai ba a sani ba ko mutumin dan achaba ne ko kuma da shi da amaryar sa sun yanke shawarar kawai su hau babur ne a ranar daurin auren su.
Kalli bidiyon a nan
Mutane sun yaba sosai da halayyar da suka nuna
Masu amfani da kafafen sada zumunta dai abin ya birge su matuka, inda suka yaba da tsantsan da kai na amaryar da har ta yarda a dauke ta a babur a ranar aurenta. Sun kuma yabawa angon bisa hikimar da ya nuna maimakon yayi abinda zai kure kan shi.
@patmore 77 ya rubuta:
“Har na fada kaunar wannan motar taka ta musamman. Ubangiji ya albarkaci aurenku.”
@cissy Akky ya rubuta:
“Wannan shine abinda muke kira da so na gaskiya da babban baki.”
@kansi44 ya rubuta:
“Ba kowa bane zai iya samar da mota ba domin zirga-zirga. Ina taya ku murnar aure.”
Ango ya fice daga gurin ɗaurin aure bayan gano Amaryar nada yara 4
A wani labarin na daban kuma, wani ango ya fice daga wurin daurin aure bayan ya gano amaryar sa nada yara hudu.
A wani ɗan gajeren bidiyo, anga yadda wani ango ya fice daga gurin ɗaurin aure, a yayin da jama’a da dama suka biyo shi suna ta ƙoƙarin bashi haƙuri. Haka nan, an hangi amaryar tana ta sharɓar kuka a yayinda wasu gungun mata ke ƙoƙarin rirriƙeta.
A wani ɗan guntun bidiyo da aka ɗora a Instagram wanda kuma ya karaɗe kafafen sadarwa na zamani, anga angon ya fito a fusace yana ta kumfar baki, a lokacin da wasu gungun mutane keta ƙoƙarin bashi haƙuri
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com