Fitacciyar mawakiya kuma mai rawa, Korra Obidi ta bayyana cewa tsohon mijinta, Justin Dean, yana bukatar kudin tallafi yayin da yake son ya amshe duk yaran, June da Athena, Vanguard ta ruwaito.
Obidi ta bayyana hakan ne a wani bidiyo da tayi a Facebook. Matar mai yara biyu ta cewa ta sanar da lauyansa cewa tsohon mijinta ya bukaci ya amshe yaran daga wurinta, amma alkali ya ki ba shi.
Korra ta kara da bayyana cewa ita ce take biyan kudin makarantar yaran tun watan Fabrairu, wanda ya kai $1800, Justin yana bukatar kudin tallafi. A cewarta:
“Yanzu na gama amsa waya daga lauyana cewa dan uwana, tsohon mijina, ya maka kara akan ayi gaggawar amshe yarana daga hannuna a ba shi, amma alkali ya ki yarda. Yana kuma bukatar kudin tallafin bayan rabuwar aure.
“Ni ce ke biyan kudin makarantar yaranmu tun watan Fabrairu har yanzu, wanda ya kai $1800 ko wanne wata, ni kadai. “Cewa yayi ina ja masa matsala a kwakwalwa, don haka yana bukatar kudin tallafi.
“Ina godiya ga Alkalin da mutanen da ke mara min baya a wannan lokacin mai tsanani. Ina tunanin lokacinmu yayi na maka shi kara saboda bacin suna.”
Mata ta da kanta ta nemi aure na – makahon da ya auri zuƙeƙiyar mata
Wani makaho mai suna Ademola Adeleke ya bayyana cewa kyakkyawar matar shi da ya aura, itace da kanta ta nemi auren shi. Ya bayyana cewa a hakan shi ta ganshi kuma ya birgeta.
Yana jin daɗin zama da matar
Adeleke ya ƙara da cewa yana jin daɗin zama da matar shi saboda ya yarda da ita sosai kuma yana samun natsuwa a ran shi a duk lokacin da yake tare da ita, kamar yadda majiyar mu ta legit ta wallafa.
Ya kuma ce a lokacin da ta yanke shawarar ta aure shi, mutane da dama sunyi ƙoƙarin zuga ta akan kada ta aure shi. Matar duk bata maida hankali akan masu faɗa mata kada ta auri shi ba.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com