LabaraiWata mata ta kashe kanta saboda mijin ta zai...

Wata mata ta kashe kanta saboda mijin ta zai ƙara aure

-

- Advertisment -spot_img

Ana zargin cewa wata mata mai suna Yetunde Folorunsho ta kashe kanta ta hanyar shan gubar maganin ƙwari domin ta hana mijin ta mai suna Dare Araoje ƙara aure.

Lamarin ya faru a Ilorin jihar Kwara

Dailytrust ta wallafa cewa wannan lamari dai ya faru ne a garin Ilorin na jihar kwara inda matar wacce take da ‘ya ‘ya guda biyu tare da mijin ta suke zaune.

Mai magana da yawun hukumar ‘yan sanda na jihar kwara Ajayi Okasanmi ya shaidawa manema labarai cewa binciken da suka gudanar akan gawar matar ya tannatar da cewa lallai ta sha maganin ƙwarin nan ne da ake kira da ‘sniper’ wanda shine yayi ajalin nata.

Matar, wacce tayi digirin ta a bangaren nazarin yaruka, wacce kuma ‘yar asalin jihar Osun ce ta mutu ne a lokacin da ake kan hanyar kaita asibitin gwamanti dake garin Ilorin.

Mutuwar matar ta kawo ruɗani a tsakanin dangogi biyu

Sai dai kuma lamarin ya kawo ruɗani a tsakanin dangin matar da kuma dangin mijin nata, inda danginta ke zargin cewa mahaifiyar mijin ce ta sanya mata gubar a abinci sabili da saɓanin addini da suka samu.

Majiyar tamu ta ƙara da cewar a can baya mata ta kasance tana bin addinin Kiristanci, amma daga bisani sai ta karɓi Musulunci, matakin da kwata-kwata bai yima ‘yan uwanta daɗi ba.

‘yan uwanta sun tsayu akan cewa lallai fa su sun tabbatar da cewa matar ba zata iya kashe kanta ba, illa iyaka dai kawai an kashe ta ne.

Sai dai kuma majiyar tamu ta bayyana cewa mazauna yankin da lamarin ya faru sun shaida musu cewa fa lallai matar ta kashe kanta ne ta hanyar shan guba saboda saɓanin da suka samu da mijin ta kan batun ƙara aure da yayi.

Matar ta tabbatar da haka kafin mutuwar ta

Wani ɗan uwan mijin mai suna Lagbe Araoje ya shaida ma ‘yan jarida cewa matar ta ɗan samu saɓani da mijin amma kuma an sasanta su, tunda har waya ma mijin ya siya mata bayan nan.

“Bayan nan sai ta shiga gida. Can ba da daɗewa ba sai ga mijin mata ya fito yana kuka ya na neman jama’a su kawo mishi ɗauki matar shi na ta amai. Akan hanyar mu ta zuwa asibiti ne ta roƙi mijin akan ya yafe mata domin kuwa ta sha maganin ƙwarin da ake cema ‘sniper’ .” inji shi.

Mai kyamis ɗin da ya siyar ma da matar maganin ya tabbatar ma da manema labarai cewa lallai gurin shi ta sayi maganin, sai dai bai yi zargin cewa zuwa zata yi ta sha ba.

A wani labarin kuma, kunji wata fitacciyar mawaƙiya ‘yar ƙasar Saliyo mai suna Swadu Natasha Beckley ta karɓi addinin musulunci, inda ta kuma bayyana cewa ra’ayin ta ne ta karɓi addinin tunda ta ga shi ya fiye mata.

A rana juma’a, 28 ga watan Oktoban da ya gabata ne dai mawaƙiyar ta wallafa a shafin ta na Instagram inda ta sanar da cewar ta koma addinin musulunci.

Ta ƙara da cewar sama da shekara ɗaya tana ta son ta komawa addinin Musulunci, kuma yanzu tunda ta musulunta zata yi ƙoƙarin ganin cewa ta koyi duk abubuwan da suka kamata ta koya, duk da dai cewa akwai abubuwa da yawa da ya kamata ta koya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Latest news

Ɓeraye ne su ka bushe wiwin da mu ka ƙwace mai nauyin 200kg, ‘Yan sanda

‘Yan sandan Indiya sun koka kan yadda beraye su ka lamushe wiwi mai nauyin 200kg bayan sun kwace ta...

Daɗi miji: Bayan an kulle shi saboda ya laƙada mata duka, matar ta yi belin mijinta

Wata mata ta yi belin mijinta bayan an kama shi sannan a sakaya shi saboda ya lakada mata na...

Wata mata ta haihu a masallacin Annabi

Wata mata cikin masu gudanar da umra ta haihu a masallacin ma'aiki dake Madinah wacce ta samu taimakon wasu...

‘Yan gida daya su 11 sun mutu bayan cin wani abinci

Aƙalla mutane 11 ne 'yan gida ɗaya aka tabbatar da sun mutu bayan cin wani abinci da ake zargin...
- Advertisement -spot_imgspot_img

Matashi ya kaɗu bayan gano cewa budurwar sa a kango take rayuwa

Wata matashi ɗan Najeriya ya shiga kaɗuwa matuƙa bayan gano cewa budurwarsa ta tsawon wata takwas a cikin wani...

An zaɓi mace musulma ‘yar majalissar jiha a Amurka

Nabeela Syed, 'yar asalin ƙasar Indiya ta kasance mace musulma ta farko da aka zaɓa a matsayin 'yar majalissar...

Must read

Ɓeraye ne su ka bushe wiwin da mu ka ƙwace mai nauyin 200kg, ‘Yan sanda

‘Yan sandan Indiya sun koka kan yadda beraye su...

Daɗi miji: Bayan an kulle shi saboda ya laƙada mata duka, matar ta yi belin mijinta

Wata mata ta yi belin mijinta bayan an kama...
- Advertisement -spot_imgspot_img

You might also likeRELATED
Recommended to you