LabaraiLabaran DuniyaKarbar addini da na yi ra'ayi na ne -...

Karbar addini da na yi ra’ayi na ne – Mawakiyar da ta karbi addinin Musulunci

-

- Advertisment -spot_img

Wata fitacciyar mawaƙiya ‘yar ƙasar Saliyo mai suna Swadu Natasha Beckley ta karɓi addinin musulunci, inda ta kuma bayyana cewa ra’ayin ta ne ta karɓi addinin tunda ta ga shi ya fiye mata.

A rana juma’a, 28 ga watan Oktoban da ya gabata ne dai mawaƙiyar ta wallafa a shafin ta na Facebook inda ta sanar da cewar ta koma addinin musulunci.

Sama da shekara ɗaya tana son karɓar musulunci

Ta ƙara da cewar sama da shekara ɗaya tana ta son ta komawa addinin Musulunci, kuma yanzu tunda ta musulunta zata yi ƙoƙarin ganin cewa ta koyi duk abubuwan da suka kamata ta koya, duk da dai cewa akwai abubuwa da yawa da ya kamata ta koya.

“Na karɓi addinin Musulunci a wannan juma’ar. Zanyi bayani nan bada jimawa ba, amma na kai tsawon shekara ɗaya da wata ɗaya ina ƙoƙarin ganin cewa nayi hakan.

“Shi yasa a wannan juma’ar kawai na yanke shawarar hakan. Duk da dai nasan da cewa ba’a dare ɗaya zan koyi komai da ya danganci musulunci ba, amma lallai zanyi iya bakin ƙoƙarina wajen ganin na koyi abubuwan da suka kamata.” inji mawaƙiyar.

An caccaki nawaƙiyar kan yanayin shigar ta

Mutane da dama sun caccake ta kan yanayin shigar ta da yadda take fitowa, sai dai mawaƙiyar tace da da sannu-sannu zata koyi komai da komai da ya kamata ta koya na addinin Muslunci.

“Ku saurara kuji, wannan sabuwar hanya ce dana ɗauka kuma nake sanar daku. Da sannu-sannu ina ƙara koyon yadda ake gudanar da addinin. Amma ina son ku sani cewa, ra’ayin ku ako da yaushe zai zama na ku ne ba nawa ba. Wannan ni ra’ayina ne da na zaɓar kaina don na cigaba da kasancewa a ciki.

Ƙungiyoyin addinin musulunci sun yaba mata

Kungiyoyi da dama na addinin musulunci sun yaba ma mawaƙiyar bisa ƙoƙarin da ta yi na karɓar addinin inda suka riƙon Allah ya tabbatar da ita akan hanya madaidaiciya.

A wani labarin na daban kuma, kunji wani makaho da ya bayyana cewa kyakkyawar matar shi da ya aura, itace da kanta ta nemi auren shi. Ya bayyana cewa a hakan shi ta ganshi kuma ya birgeta.

Adeleke ya ƙara da cewa yana jin daɗin zama da matar shi saboda ya yarda da ita sosai kuma yana samun natsuwa a ran shi a duk lokacin da yake tare da ita, kamar yadda majiyar mu ta legit ta wallafa.

Ya kuma ce a lokacin da ta yanke shawarar ta aure shi, mutane da dama sunyi ƙoƙarin zuga ta akan kada ta aure shi. Matar duk bata maida hankali akan masu faɗa mata kada ta auri shi ba.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Latest news

Ɓeraye ne su ka bushe wiwin da mu ka ƙwace mai nauyin 200kg, ‘Yan sanda

‘Yan sandan Indiya sun koka kan yadda beraye su ka lamushe wiwi mai nauyin 200kg bayan sun kwace ta...

Daɗi miji: Bayan an kulle shi saboda ya laƙada mata duka, matar ta yi belin mijinta

Wata mata ta yi belin mijinta bayan an kama shi sannan a sakaya shi saboda ya lakada mata na...

Wata mata ta haihu a masallacin Annabi

Wata mata cikin masu gudanar da umra ta haihu a masallacin ma'aiki dake Madinah wacce ta samu taimakon wasu...

‘Yan gida daya su 11 sun mutu bayan cin wani abinci

Aƙalla mutane 11 ne 'yan gida ɗaya aka tabbatar da sun mutu bayan cin wani abinci da ake zargin...
- Advertisement -spot_imgspot_img

Matashi ya kaɗu bayan gano cewa budurwar sa a kango take rayuwa

Wata matashi ɗan Najeriya ya shiga kaɗuwa matuƙa bayan gano cewa budurwarsa ta tsawon wata takwas a cikin wani...

An zaɓi mace musulma ‘yar majalissar jiha a Amurka

Nabeela Syed, 'yar asalin ƙasar Indiya ta kasance mace musulma ta farko da aka zaɓa a matsayin 'yar majalissar...

Must read

Ɓeraye ne su ka bushe wiwin da mu ka ƙwace mai nauyin 200kg, ‘Yan sanda

‘Yan sandan Indiya sun koka kan yadda beraye su...

Daɗi miji: Bayan an kulle shi saboda ya laƙada mata duka, matar ta yi belin mijinta

Wata mata ta yi belin mijinta bayan an kama...
- Advertisement -spot_imgspot_img

You might also likeRELATED
Recommended to you