Kotu ta tura wani barawo wanda ya tsere daga hannun ‘yan sanda sannan ya bayar da kyautar ankwar da aka daure shi da ita, zuwa magarkama a jihar Adamawa.
Barawon wanda ya samu ya gudu daga hannun ‘yan sandan yayi kyautar ankwar da akayi amfani da ita wajen daure shi, bayan ya samu ya gudu ya kyautar da ankwar ga abokin shi wanda shi kuma ya sayarwa da Baban Bola. Shafin LIB ya rahoto.
Yayi kyauta da ankwar da aka daure shi da ita
Barawon mai suna Dalhatu Said, an kama shi tunda farko ne bayan an kawo rahoto wurin ‘yan sanda cewa ya hada baki da wasu bata gari sun saci Talo-Talo a ranar 22 ga watan Satumba.
Sai dai ya tsallaka katangar ofishin ‘yan sandan da aka tsare shi a Sangere, a Yola, sannan yaba abokin shi kyautar ankwar wanda shi kuma ya siyar da ita ga ‘yan bola-bola.
Yadda hukuncin sa zai kasance
Bayan sake cafke shi da gurfaranar da shi a gaban kotu, mai Shari’a Ibrahim Musa Ulenda, ya yanke masa hukunci bisa laifin yin sata da kuma tserewa daga magarkama.
Kotun ta yankewa Dalhatu hukuncin shekara daya a gidan kaso ko tarar Naira dubu goma (N10,000) bisa tserewa daga hannun hukuma da kuma wani hukuncin shekara uku a gidan kaso ko tarar Naira dubu hamsin (50,000) bisa aikata laifin sata. Alkalin ya kuma umarce shi da ya biya diyyar Naira dubu bakwai (N7,000).
Yadda wasu matasa suka tasa wa barawo taliya, bayan ya lamushe suka hau jibgarsa
A wani labarin na daban kuma, wasu matasa sun yiwa wani barawo abin arziki kafin daga baya suka hada masa na jaki.
An ba wa wani da ake zargin barawon kebur ne kwanon taliya, yayin da ake mishi horo a yankin Agorogbene na karamar hukumar Sagbama dake jihar Bayelsa, LIB ta ruwaito.
An kama wanda ake zargin, Preye Ayase da abokin harkarsa, Ringo Tareladei dumu-dumu suna satar keburan wutar da ke sada Ogobiri da yankin Agorogbene cikin Sagbama a ranar Laraba, 20 ga watan Afirilu.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com