35.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Ba ni bane na fasa wa Sule Garo baki, zamewa yayi ya a ƙasa, Hon. Ado Doguwa

LabaraiBa ni bane na fasa wa Sule Garo baki, zamewa yayi ya a ƙasa, Hon. Ado Doguwa

Honarabul Ado Doguwa ya ce ba shi bane ya fasa wa Sulen Garo baki, a cewarsa zamewa yayi ya fadi sakamakon ruwan da ke cikin kofin shayin da ya zube.

Tun jiya ake ta yada maganganu da tataburza akan yadda rikici ya barke tsakanin shugaban masu rinjaye na majalisar Jihar Kano da kuma dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar APC, Ado Doguwa.

An dinga yada cewa Ado Doguwa ya jefi Sule Garo da kofin shayi wanda yayi sanadiyyar fasa masa baki, wanda Doguwa ya musanta wannan zargin.

A wata tattaunawa da BBC Hausa tayi da shi ya ce ya shiga gidan Sule Garo ne inda ya tarar Sule da wasu Kwamishinoni da masu fadi a ji a APC ta Jihar Kano su na taro.

A cewarsa ya tambayi Garo dalilin da yasa ba a gayyace su ba, sai yace ba su ga damar gayyatar tasu ba.

Wannan maganar ce tayi matukar hassala shi ya daga masa murya. Garin haka ne wani kofin shayi ya fadi ya fashe, ruwan da ke cikin kofin shayin ne ya janyo Garo ya zamiye ya fadi har ya fasa baki.

A bangaren Sule Garo, ya ce tabbas Doguwa ne ya jefe shi da kofin shayin. Ya ce ya shigo ne ya tarar su na taro inda ya bukaci idan kudi ne a raba da su, shi kuma yace ba kudi bane.

Bayan nan ne ya jefe shi da kofin shayin. Mu na fatan Ubangiji ya daidaita su. Ameen.

Budurwa ta fasa auran angonta ana saura kwana uku daurin aure, ta bayyana dalilan ta

Wata budurwa ta fasa auran mijin da zata aura ana saura kwana uku a daura musu aure.

Wata shahararriyar mai watsa labarai, Amanda Chisom, itace ta sanya hoton wallafar da budurwar tayi na cewa ta fasa auran.

A cikin rubutun da budurwar tayi a shafin Twitter, tace koda yaushe mijin da zata aura yana ce mata kudin sa na a asusun da ba a tabawa. Jaridar Legit.ng ta rahoto.

Budurwar ta fasa auran

Duk da rokon da budurwar ta sha yi, saurayin yace zai biyata duk abinda ta kashe a bikin. Daga karshe dai ta fasa auran bayan ta samu shawara daga wajen wani masani kan lamuran aure.

A kalamanta:

“Wannan mutumin bai bayar da ko asi ba kuma daurin auren saura kwana uku, yana ta cewa kudin sa na asusun da ba a tabawa, sannan zai biya ni daga baya.”

Budurwar ta fasa auran

Duk da rokon da budurwar ta sha yi, saurayin yace zai biyata duk abinda ta kashe a bikin. Daga karshe dai ta fasa auran bayan ta samu shawara daga wajen wani masani kan lamuran aure.

A kalamanta:

“Wannan mutumin bai bayar da ko asi ba kuma daurin auren saura kwana uku, yana ta cewa kudin sa na asusun da ba a tabawa, sannan zai biya ni daga baya.”

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana raayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe