24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Mata ta da kanta ta nemi aure na – makahon da ya auri zuƙeƙiyar mata

LabaraiMata ta da kanta ta nemi aure na - makahon da ya auri zuƙeƙiyar mata

Wani makaho mai suna Ademola Adeleke ya bayyana cewa kyakkyawar matar shi da ya aura, itace da kanta ta nemi auren shi. Ya bayyana cewa a hakan shi ta ganshi kuma ya birgeta.

Yana jin daɗin zama da matar

Adeleke ya ƙara da cewa yana jin daɗin zama da matar shi saboda ya yarda da ita sosai kuma yana samun natsuwa a ran shi a duk lokacin da yake tare da ita, kamar yadda majiyar mu ta legit ta wallafa.

Ya kuma ce a lokacin da ta yanke shawarar ta aure shi, mutane da dama sunyi ƙoƙarin zuga ta akan kada ta aure shi. Matar duk bata maida hankali akan masu faɗa mata kada ta auri shi ba.

Adeleke ya yaba ma matar tashi inda ya bayyana ta a matsayin mace mai ra’ayin kanta, mai kaifin tunani, wacce kuma bayan auren nasu take ƙoƙarin yin duk abinda ya shafi walwala da jin daɗin shi.

Ba’a makaho aka haife shi ba

Makahon, wato Ademola Adeleke an haife shi lafiya lau da idanun shi kamar dai sauran mutane. Sai dai a lokacin da yakai shekara 16 sai wannan matsalar ta makanta ta same shi.

Abinda Ya baiwa mutane da dama mamaki shine yadda yayi ƙoƙarin yin karatun zamani duk da wannan hali na malanta da ya tsinci kan shi a ciki, wanda masu idanun ma sai sun yi da gaske, duba da tsarabe-tsaraben dake tattare da hakan.

Makahon wanda ɗan garin Ibadan ne jihar Oyo ya bayyana cewa bai yi ƙasa a gwuiwa ba wajen jajircewa don ganin ya cimma muradun shi na yin karatu mai zurfi. Yayi digirin shi a ɓangaren aikin jarida, wanda ya ga ma shi cikin nasara.

Da aka tambaye shi ko ta yaya ya rinƙa yin karatu, makahon ya bayyana cewa ya na zuwa aji ne ya zauna ya saurari farfesoshi. Sannan ya bayyana cewa an koya mishi yadda ake amfani da injin rubutu da kuma na’ura mai ƙwaƙwalwa, saboda haka ya samu ƙwarewa.

Ya ƙara da cewar yana amfani da abun naɗar murya wajen ɗaukar darasi, wanda idan ya koma gida yake saurara. Idan kuma anzo wajen jarabawa, masu tsaron jarabawar na karanto mishi tambayoyin wanda shi kuma yake rubuta wa a cikin na’urar shi.

Ya samu aiki bayan kammala karatu

Bayan kammala karatun na shi, makahon ya samu aikin koyarwa da gwamnatin jihar Oyo inda yake dauke shi malamin koyar da nahawun turanci. Yace yana samun dogaye daga cikin ɗaliban shi da suke mishi rubutu a kan allo a yayin da yake gudanar da darasi.

Ya yaba ma kyakkyawar matar tashi sosai bisa yadda take fara gabatar da buƙatun shi kafin nata, ya kuma ƙara da cewa matar tashi abin dogaron shi ce.

A wani labarin na daban kuma, wata mata ta ce bai kamata amare su rinƙa kishi ko gasa da uwargida ba.

Shahararriyar mai amfani da kafar sada zumunta ta facebook Jamila Ibrahim ta bayyana cewa ba daidai bane amare su riƙa yin kishi ko gasa da uwargida a gidajen mazajen su ba domin kuwa ita tasha wahalar mijin.

Jamila wacce ita ce keda dandalin Facebook na home of Solace ta bayyana haka ne a wani rubutu data wallafa a shafinta da safiyar Lahadin nan.

Tace tana mamakin yadda wasu amaren ke yi na yanda suke ƙoƙarin nuna kishi da gasa da uwargida wacce su zuwa suka yi suka tarar da ita da mijin, ba tare da sun san irin faɗi tashin da ta sha tare da shi ba.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe