24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

An cafke ‘yar aiki na kokarin sanya guba a ruwan shan matar gida

LabaraiAn cafke 'yar aiki na kokarin sanya guba a ruwan shan matar gida

Asirin wata ‘yar aiki ya tonu yayin da aka kamata tana kokarin sanya maganin kwari a ruwan shan uwargidanta.

A wani bidiyo da nan da nan  ya karade shafukan sada zumunta, an ga ‘yar aikin ta durkusa kan guiwoyinta tana amsa tambayoyin uwargidan na ta bayan an yi ram da ita. Kamar yadda muka samo daga shafin Bestshowbiz.

Ta bayyana dalilin ta na kokarin yin kisan kai

‘Yar aikin gidan ta bayyana cewa tayi alkawarin sai ta halaka duk wanda ya gaya mata wata maganar da ba tayi mata dadi ba a rai.

A cewar ta, ta cire ‘yan makullan dakin matar gidan daga wurin da aka saba ajiye su, ta shiga dakin sannan ta sanya gubar a cikin ruwan shan ta.
Sai dai tayi rashin sa’a domin duk wannan tuggun da take shiryawa an dauka a kyamara yayin da take aikatawa.

Ba a san takamaimai dalilin da yasa take kokarin halaka matar gidan ba

Wannan lamarin dai ya sanya mutane da dama tunanin ko wane irin abu matar gidan take yiwa ‘yar aikin da har ya sanya tayi tunanin ta cutar da ita, yayin da wasu kuma sun goyi bayan matar gidan inda suka bukace ta da ta gaggauta korarta daga gidan.

Wasu daga cikin ‘yan Najeriya na goyon bayan matar gidan inda suka bata shawarar da ta koreta daga gidan ba tare da bata lokaci ba.

Kotu ta yanke wa wata ‘yar aiki hukuncin kisa bisa laifin kashe mahaifiyar tsohon gwamna jihar Edo

A wani labarin na daban kuma, kotu ta yankewa wata ‘yar aiki hukuncin kisa bisa laifin halaka mahaifiyar tsohon gwamna.

An yanke wa Miss Dominion Okoro, ‘yar aiki mai shekaru 25 hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin kashe Madam Maria Oredola Igbinedion, mahaifiyar tsohon gwamnan jihar Edo, Cif Lucky Igbinedion.

Nigerian Tribune ta ruwaito cewa Mai shari’a Efe Ikponmwoba na wata babbar kotun jihar Edo shi ne ya yanke hukuncin a ranar Talata, 21 ga watan Yuni.

Rahotanni sun bayyana cewa an samu ‘yar aikin da laifin kashe Madam Igbinedion mai shekaru 85.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe