34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

An kwashi ƴan kallo bayan bokanya ta faɗa gidan ‘yan damfarar yanar gizo, tana biɗar kasonta

LabaraiAn kwashi ƴan kallo bayan bokanya ta faɗa gidan ‘yan damfarar yanar gizo, tana biɗar kasonta

Wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumuntar zamani an ga yadda wata bokanya ta kai samame gidan wasu ‘yan damfarar yanar gizo, LIB ta ruwaito.

Kamar yadda bidiyon ya nuna, dama can bokanyar ta yi musu aiki kuma a cewarta ta binciko kudaden da su ka samu.

‘Yan damfarar wadanda aka fi sani da ‘yan Yahoo, ta yuwu sun bata wani abu kafin tayi musu aiki, daga bisani kuma taga ta yi musu a arha.

A bidiyon an ji inda ta balle rigima tana cewa tsafinta ya nuna mata ko nawa matasan su ka samu a damfarar. Hakan yasa ta afka har gidansu don ta amshi nata kason.

Ga bidiyon:

Kowa sai ya gane kurensa a Najeriya, Cewar bokanyar da ‘yan sanda su ka kama wa makada

Wata bokanya mai suna Ajefunke3 a TikTok ta dauki tsatstsauran mataki bayan ‘yan sanda sun kama wasu makadanta. A wani bidiyo da ya dinga yawo, ta bayyana wata ta yi tsafe-tsafenta a wurin wani tafki yayin da ‘yan sanda su ka kama mata makada, Legit.ng ta ruwaito.

A cewarta, bayan sun kama makadan, ta tattaro makadanta inda su ka afka ofishin ‘yan sanda don su samo mutane. Ta ce wajibi ne jami’an su gane kurensu akan mummunan aikin da su ka yi mata.

Kamar yadda ta bayyana da harshen yarabanci:

Kun ganni nan a ofishin ‘yan sanda. Ni bokanya ce kuma ba na tsoron kowa sai Ubangiji. Idan ban shiga hakkinka ba, baba so ka shiga nawa.

Yan sandan Najeriya sun shiga gonata kuma sai sun gane kurensu. Yanzu haka ina ofishin ‘yan sanda. Ni da bokaye irina mun daura dammarar yakarsu.

Kila kun ji labarin yadda aka kama Ajafunke. Tabbas, kafin in dawo rafi, ‘yan sanda sun kama min makada na ba tare da sun yi musu komai ba.

Na je da karfin ikona na kwato su. Ba su isa su rike min mutane na ba. Saboda nasan yadda zan bullo musu.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe